Yan dagajin Malamai ne ke janyo mana rikici a Najeriya – Sultan

Yan dagajin Malamai ne ke janyo mana rikici a Najeriya – Sultan

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa wasu tsirarun yan dagajin malamai daga bangaren addinin Musulunci da kiristanci ne ke janyo rikici a tsakanin al’ummar Najeriya tare da tayar da zauni tsaye a kasar.

Sarkin ya bayyana haka ne a ranar Talata 8 ga watan Janairu a garin Auchi na jahar Edo, inda aka gudanar da bikin ranar Auchi, inda yace babu tilastawa a cikin addinin Musulunci, kamar yadd majiyar Legit.com ta ruwaitoshi yana fada.

KU KARANTA: Ganduje zai biya N30,600 a matsayin karancin albashin ma'aikata

Sultan ya samu wakilcin mai martaba Sarkin Keffi, Alhaji Shehu Chindo Yamusa III ne, wanda yace ire iren malaman nan suna yin munanan wa’azi ga mabiyansu ne, musamman irin wa’azin da ka iya tunzurasu da ga tayar da rikici, duk da cewa hakan bai dace da manyan addinan biyu ba.

Da wannan ne Sultan yayi kira ga mabiya addinin Musulunci da Kiristoci dasu kasance masu girmama addinan junansu, bai kamata wani ya tilasta ma waninisa addininsa ba, walau Musulunci ko Kiristanci.

“Ya kamata Musulmai su nemi ilimi na gaske domin su fahimci yadda zasu tasan ma matsala a duk lokacin da ta taso, abin haushi ne yadda aka mayar da ilimin addinin Musulunci baya, duk da cewa ilimin addinin Musulunci shine ilimi mafi kyawu.” Inji shi.

Daga karshe mai alfarma sarkin Musulmi yayi kira ga nagartattun Malaman addini da na Kiristanci dasu jajirce wajen karantar da mabiyansu kyawawan dabi’u, halaye da tarbiyya, sa’annan yayi kira ga yan Najeriya dasu baiwa gwamnati goyon baya a kokarinta yaki da rashawa da matsalolin tsaro.

Shima a nasa jawabin, gwamnan jahar Edo, Godwin Obaseki, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Philip Shuaibu ya yaba ma Sarkin Auchi, Otaru Auchi, Aliru Momoh Ikelebe III, sakamakon rawar da yake takawa wajen tarbiyyantar da jama’an masarautarsa.

A nasa jawabin, Otaru Auchi ya bayyana cewa suna shirya wannan taro ne a shekara shekara ne domin su bayyana godiyarsu ga Allah, tare da kara ma kananan yara kwarin gwiwar neman ilimin addinin Musulunci, tare da haddar Al-Qur’ani.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel