Hatsarin jirgi: An yiwa sojojin da suka mutu a yaki da Boko Haram birnewar girma, bidiyo

Hatsarin jirgi: An yiwa sojojin da suka mutu a yaki da Boko Haram birnewar girma, bidiyo

A yau Talata 8 ga watan Janairun 2019 ne aka yi jana'izar dakarun sojojin saman Najeriya 5 da su kayi hatsari a ranar Laraba da ta gabata a yayin yaki da mayakan Boko Haram da a jihar Borno.

Sojojin biyar sunyi hatsari ne a jirgin yaki mai saukan angulu kirar Mi-35M a yayin da suke tallafawa dakarun sojin Najeriya na Bataliyar 145 a garin Damasak da ke jihar Borno.

An birne sojojin makabartar kasa da ke Abuja.

Anyi jana'izar sojojin saman Najeriya 5 da su kayi hatsari yayin yaki da Boko Haram, hotuna

Anyi jana'izar sojojin saman Najeriya 5 da su kayi hatsari yayin yaki da Boko Haram, hotuna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Idan Buhari ya fitar da sunayen barayin gwamnati, 'yan Najeriya zasu ji kamar su kashe su - Dan majalisa

Sojojin da suka rasu sune Flight Laftanat Perowei Jacob; Flight Laftanat Kaltho Paul Kilyofas; Saja Auwal Ibrahim; Lance Corporal Adamu Nura da Meshack Ishmael.

Wadanda suka hallarci jana'izar sun hada da shugabanin sojoji da suke aiki da wadanda su kayi murabus tare da abokai da iyalan sojojin.

An musu birnewar ban girma irin wadda ya dace da dakarun soji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel