Zan bar gadon tsarkakken zabe na adalci a Najeriya - Buhari

Zan bar gadon tsarkakken zabe na adalci a Najeriya - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya ce zai bar gadon tabbatar da kwararar romomn dimokuradiyya ta hanyar ingancin zabe na gaskiya da adalci

- Shugaban kasar ya ce ingancin zaben kasar nan ya ci gaba da habaka tun bayan zaben 2015

- Ya ce bajintar jam'iyyarsa ta APC bisa kujerar mulki ta cimma nasara ta inganta ci gaban kasa ta kowace fuska

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce tsarkakken zabe na adalci shine babban ginshiki kuma tubalin gina kyakkyawar siyasa mai tasirin gaske wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban kowace al'umma.

Buhari kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito ya bayyana cewa, wannan babban ginshike na tabbatar da kyakkyawan zaben na tsantsar adalci shine tubalin da zai assasa a matsayin gado da bari a kasar nan.

Shafin jaridar Vanguard ya ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari ya yi furucin hakan ne yayin kaddamar da cibiyar yakin neman zaben jam'iyyar sa ta APC a yau Litinin cikin babban birnin kasar nan na tarayya.

Shugaba Buhari ya lura da yadda ingancin zabukan kasar na ke ci gaba da habaka tun a shekarar 2015 tare da zagwanyewar ababen da ke haddasa matsalolin da suka tunkari zabukan kasar nan a baya.

Zan bar gadon tsarkakken zabe na adalci a Najeriya - Buhari

Zan bar gadon tsarkakken zabe na adalci a Najeriya - Buhari
Source: Depositphotos

Ya kuma jaddada dukufar sa ta jajircewa bisa tabbatar da kyakkyawan zabe na gaskiya da adalci da ya tsarkaka daga kowane nau'i na magudi da rashin gaskiya. Ya kuma ce zai tabbatar da ci gaba da kwararar romon dimokuradiyya ta hanyar barin kyakkyawan gado a gwamnatin kasar nan.

KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Borno ya fashe da hawaye yayin ganawa da Buhari kan rikicin Boko Haram

Kazalika shugaban kasar ya bayar shaidar sa ta yadda jam'iyyar mai ci ta APC ta cimma nasara wajen tabbatar da zaman lafiya da adalci, habakar tattalin arziki gami da ci gaban kasa ta kowace fuska.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, a yau shugaban kasa Buhari ya mika ragamar jagorancin kungiyar yakin neman zaben sa a hannun tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel