Kungiyar Boko Haram ta aika sako ga matasan Baga da Kuyawa a Borno

Kungiyar Boko Haram ta aika sako ga matasan Baga da Kuyawa a Borno

A kasa da kwanaki 10 da kama garuruwan Baga, Doron Baga, Kross Kauwa, Bunduran, Kekeno da Kukawa a jihar Borno, mayakan Boko Haram sun fara kira ga matasan garuruwan da su shiga kungiyar.

Matasan yankin da suka bar garuruwan zuwa Monguno don neman tsira ne suka sanar da hakan.

Domin bawa irin wadannan matasa da jama'ar garuruwan da abun ya shafa kwarin gwuiwa, gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya kwana guda a garin Monguno yayin hutun karshen mako.

Dakarun soji sun yi nasarar dakile harin da mayakan Boko Haram suka kai a yunkurinsu na son kama garin Monguno a satin da ya gabata.

Sai dai duk da mayakan na Boko Haram basu samu nasara ba, mutane da dama dake garin na Monguno sun gudu zuwa Maiduguri domin samun kwanciyar hankali, amma ziyarar gwamnan ta saka da dama sun koma gidajensu kuma sun cigaba da harkokin rayuwa na yau da gobe.

Kungiyar Boko Haram ta aika sako ga matasan Baga da Kuyawa a Borno
Mayakan kungiyar Boko Haram
Asali: UGC

Sai dai har yanzu mayakan Boko Haram din na cigaba da kira ga matasan garuruwan Baga, Doron Baga da sauransu da su shiga kungiyar.

Wani daga cikin matasan garin Baga da ya nemi a boye sunansa ya shaidawa majiyar mu cewar ya gudu daga garin bayan ya ki amincewa da tayin 'yan Boko Haram na shiga kungiyar su.

"Sun same ni kamar yadda suke samun matasa a garinmu a kan bukatar su shiga kungiyar su. Basu nuna niyyar tilasta min sai na shiga kungiyar ba amma sai umarce ni na bar garin kuma kar na kara dawowa tunda ba zan shiga kungiyar su ba.

DUBA WANNAN: Tsaro: Rundunar soji ta mika mutane 71 ga rundunar 'yan sanda a Adamawa, hoto

"Ban yi tunanin zasu bar ni na tafi ba bayan na nuna bani da sha'awar shiga kungiyar ba domin mun sha samun labarin yadda suke yi ga duk wanda ya ki amincewa da tayin zama dan kungiyar Boko Haram. Nayi tafiyar kafa ta tsawon kwana biyu daga Baga domin tsira da rai na," a cewar matashin.

Matashin da kafar sa ta kumbura saboda tafiyar kafa mai tsayi ya cigaba da cewa, "sabanin tsoron 'yan Boko Haram da muke ji daga labaransu da muke ji, wannan karon sun nuna hali daban bayan sun kama garinmu a satin da ya wuce don suna zaune da jama'ar gari lafiya, har siyayya suke yi a wurin 'yan kasuwar da basu bar gari ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng