Cin amana: Budurwa tayi aure da wani saurayi bayan an tura saurayinta soja Borno

Cin amana: Budurwa tayi aure da wani saurayi bayan an tura saurayinta soja Borno

Wani sojan Najeriya da ke filin daga a yankin Arewa maso gabashin Najeriya bayar da labarin yadda ya gano Budurwarsa da ya bari a gida tayi aure ba tare da ya sani ba kwatsam sai dai ya ga hotunan aure a shafunkan sada zumunta.

Wani sojan Najeriya mai suna Emmy Benison ya yi amfani da shafinsa na sada zumunta inda ya bayar da labarin yadda budurwarsa da suka kwashe shekaru hudu suna soyaya tayi aure ba tare da ya sani ba.

Benson ya ce sun kwashe shekaru biyu ba su hadu ba amma yana sa ran da zarar ya dawo ya garzaya wajen ta domin su cigaba da soyaya kamar yadda suka dade suna yi.

Yadda budurwar wani soja tayi aure ba tare da saninsa ba yayin da yake yaki da Boko Haram

Yadda budurwar wani soja tayi aure ba tare da saninsa ba yayin da yake yaki da Boko Haram
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan ta'addan sun kwace iko da kananan hukumomi 8 a jihar Katsina

Sai dai ya yi matukar mamakin ganin hotunan auren da wani mutum ba tare da ta sanar dashi cewa za tayi aure ba.

A cewarsa, ya yi kuka amma dole ya jajirce ya cigaba da aikinsa saboda babu damar karayar zuciya a filin daga.

Ga sakon da ya rubuta a shafinsa na Instagram: 'Mun fara soyaya shekaru hudu da suka wuce amma nayi shekaru biyu ban dawo gida ba. Bata fada min cewa ba zata iya jira na ba. Fata ne shine wata rana zan dawo gida kuma in faranta mata rai amma yau kwatsam sai na farka naga hotunan auren ta. Na zubda hawaye amma dole na jajirce domin ba a karayar zuciya a filin daga.'

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel