Iyalan marigayi Shehu Shagari sun bayyana bacin rai game da yadda Buhari ya cutar da mahaifinsu

Iyalan marigayi Shehu Shagari sun bayyana bacin rai game da yadda Buhari ya cutar da mahaifinsu

Guda daga cikin manyan yayan tsohon shugaban kasa, marigayi Alhaji Shehu Shagari, Aminu Shagari ya bayyana baci ransa da wasu abubuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi, wanda a cewarsa hakan cutarwa ne ga mahaifinsu, kuma ya basu kunya matuka.

Aminu ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da jaridar Punch, inda yace Buhari ya basu kunya matuka game da irin abubuwan da suka faru kafin mutuwar mahaifinsu da kuma bayan mutuwar tasa.

KU KARANTA: Za ayi garkuwa da gwamnonin jihohin Najeriya guda 5 – Wani Gwamna ya bayyana ma Sojoji

Iyalan marigayi Shehu Shagari sun bayyana bacin rai game da yadda Buhari ya cutar da mahaifinsu
Buhari, Aminu da Shagari
Asali: UGC

Babban abin bakin cikin da Buhari yayi ma Shagari shine yadda ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi masa juyin mulki a karshen watan Disambar shekarar 1983 jim kadan bayan ya sake cin zabe karo na biyu, inda Aminu ya bayyana hakan a matsayin cin amanar mahaifinsa daga wajen mutanen daya amincie mawa.

“Duk da cewa mahaifina ya yafe ma wadanda suka hambarar da gwamnatinsa, amma fa kamar duk wani mutum da ka sani, bai manta ba har rasuwarsa, kuma har ya rasu bai samu kulawar data dace da shi ba, musamman daga wadanda suka ci amanarsa ta hanyar juyin mulki duk da cewa basu kamashi da wata laifi ba.

“Haka zalika mun baiwa Buhari gudunmuwa wajen zama shugaban kasa, amma daya ci zabe bai sake waiwayar iyalanmu ba, ina ganin ya kamata ace ya kula damu sosai, musamman yadda ya yi ma mahaifinmu juyin mulki a baya duk cewa ya amince musu.

“Kuma a lokacin daya kawo mana ziyarar ta’aziyya bamu ji ya fadi maganganun da zasu kwantar mana da hankali ba, babu abinda yace bayan sanya hannu da yayi akan littafin masu ta’aziyya, na ji kunya sosai, domin na dauka a matsayinsa na Musulmi zai rubuta ‘Allah Ya jikansa…. Amma ba ko daya.” Inji shi.

A ranar 28 ga watan Disambar 2018 ne Shagari ya rasu yana dan shekara 93, aka yi jana’izarsa a garin Shagari dake jahar Sakkwato, sai dai Buhari bai halarci jana’izar ba, amma daga bisani ya kai ziyarar ta’aziyya, sa’annan ya bada umarnin sauke tutocin Najeriya zuwa rabi, kuma yayi alkawarin raya sunan marigayi Aliyu Usman Shehu Shagari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel