An kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan

An kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan

Wasu batagari daga wasu sassan garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun saka wa gidaje fiye da 20 wuta a wani rikici tsakanin kungiyoyin 'yan daba a yankin Idi Arera.

Daga cikin gine-ginen da 'yan dabar suka saka wa wutar akwai shagunan masu dinki, shagunan sayar da lemukan roba, shagunan kayan wutar lantarki da na abinci da na kayan sawa da sauran su.

Majiyar Legit.ng ta shaida mata cewar barkewar rikicin na safiyar yau, Lahadi, ya biyo bayan rigingimun dake faruwa ne tsakanin kungiyoyin 'yan dabar.

Rahotanni sun bayyana cewar ba don dagewar 'yan kungiyar bijilanti da wasu jama'ar unguwa ba yayin rikicin, da barnar da 'yan dabar zasu yi sai ta fi haka.

A wani labarin na Legit.ng daga jihar ta Oyo, kun ji cewar Tsohon Sanata kuma tsohon gwamnan jihar, Rashidi Ladoja, ya ce ya yi ritaya daga yin takarar kowacce kujera a Najeriya saboda wahalar da ya ce ya sha lokacin da yake gwamna.

An kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan
An kona gidaje da shaguna a sabon rikicin da ya barke a Ibadan
Asali: Twitter

Ladoja, mai rike da mukamin Olubadan na kasar Ibadan, ya zama gwamna a jihar Oyo a tsakanin shekarar 2003 zuwa shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar PDP. an tsige shi a watan Janairu na shekarar 2006, amma kotu ta mayar da shi a shekarar a watan Disamba na shekarar.

DUBA WANNAN: Kwamandan Boko Haram ya fadi gari da malamin da ya saka shi a kungiyar

Da yake wannan kalami a yau, Asabar, Ladoja ya bayyana cewar ya yanke shawarar yin bankwana da takara ne saboda samun lokacin kulawa da bukatun iyalinsa.

A hirar sa da manema labarai a garin Igholo, hedkwatar karamar hukumar Oorelope, Ladoja ya ce, "kadan ya rage na manta da iyalina lokacin da nake gwamnati. Mun yi iya bakin kokarinmu, amma ni kam ba zan kara yin takara ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel