Ranar da aka yi wa Buhari ihu a Majalisa, ban zo aiki ba – Sanata Melaye

Ranar da aka yi wa Buhari ihu a Majalisa, ban zo aiki ba – Sanata Melaye

Mun ji cewa Sanatan da ke wakiltar yankin jihar Kogi ta yamma, Dini Melaye, ya bayyana cewa ba ya cikin ‘yan majalisar tarayyar da su ka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu kwanakin baya.

Ranar da aka yi wa Buhari ihu a Majalisa, ban zo aiki ba – Sanata Melaye
Dino Melaye ya cire kan sa daga cikin masu yi wa Buhari ihu
Asali: Twitter

Sanata Dino Melaye ya karyata rade-radin da aka dade ana yadawa inda ya tabbatar da cewa ba ya cikin majalisar tarayya a lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2019 a karshen watan da ya gabata.

Fitaccen Sanatan yace don haka ba ya cikin wadanda su ka rika yi wa Buhari a lokacin da yake jawabi a gaban ‘yan majalisar kasar. Sanatan na jihar Kogi yayi wannan jawabi ne ta hannun wani Hadimin sa, Gideon Ayodele.

KU KARANTA: Yadda Dino Melaye ya fito daga gidansa, ya zube warwas a kasa

Gideon Ayodele ya bayyana cewa da farko yayi watsi da rade-radin, amma yace dole ta sa ya fito yayi magana, ganin yadda rade-radin ya bi Duniya. Mista Ayodele ya kalubalanci masu yada wannan magana su kawo hujja.

Idan ba ku manta ba, ‘yan adawa yi wa shugaban kasar ihu a Ranar 19 ga watan Disamba lokacin da ya mikawa majalisa kundin kasafin kudin bana. ‘Yan majalisun APC sun yi kokarin maidawa masu hamayyar martani.

‘Dan majalisar wanda ya saba sukar Buhari, tun kafin ya sauya-sheka zuwa PDP, yace karya ake yi masa da aka ce yana cikin wadanda su ka rika yi wa shugaban kasa ihu, inda yace bai ma halarci zaman da aka yi a wannan ranar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel