Handama da babakere: Attahiru Bafarawa ya shigar da karar Alu Wammako gaban EFCC

Handama da babakere: Attahiru Bafarawa ya shigar da karar Alu Wammako gaban EFCC

Tsohon gwamnan jahar Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi tattaki kafa da kafa zuwa gaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, inda ya nemi ta kama tsohon gwamnan jahar, Sanata Alu Wammako saboda a cewarsa barawo ne.

Legit.com ta ruwaito a shekarar data gabata ne dai kotu ta wanke Bafarawa daga zarge zarge da tuhume tuhumen badakalar satar kudi da almubazzaranci da hukumar EFCC ke yi masa, don haka a yanzu ya samu bakin shigar da karar Alu Magatakardan Wammako.

KU KARANTA; Mutuwar Shagari: Sarkin Kano, Ganduje da Tinubu sun kai ziyarar ta’aziyya Sakkwato

Handama da babakere: Attahiru Bafarawa ya shigar da karar Alu Wammako gaban EFCC

Bafarawa da Alu
Source: UGC

Kafa da kafa Bafarawa ya kai karar Wammako wanda ya zama gwamnan jahar Sakkwato bayan kare wa’adin mulkin Dalhatu Bafarawa, inda ya isa ofishin EFCC dake jahar Sakkwato, kuma ya samu kyakkyawar tarba daga babban jami’in ofishin hukumar, Ahmed Lateef.

A jawabin Bafarawa, ya nemi hukumar EFCC ta kaddamar da bincike akan wasu makudan kudade da yace ya bari a asusun gwamnatin jahar bayan wa’adin mulkinsa ya kare a matsayin gwamnan jahar Sakkwato.

Bafarawa yace a lokacin daya fita daga gidan gwamnati a shekarar 2007, ya bar kimanin adadin kudi da suka kai naira biliyan goma sha uku (N13,000,000,000) a lalitar gwamnatin jahar, don haka ya kamata EFCC ta gayyaci Wammako don ya amsa yadda yayi da kudaden nan.

Tsohon gwamnan ya farfasa yadda kudaden suka kai naira biliyan goma sha uku, inda yace daga ciki akwai naira biliyan goma sha daya da miliyan dari takwas daya bari a lalitar gwamnatin, naira miliyan 500 na cibiyar karatun Al-Qur’ani ta Muhammadu Maccido dakuma karafan rodi da kudinsu ya kai naira biliyan daya (N1,000,000,000).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel