Tabdijam! Buhari da Osinbajo zasu kashe N1.4bn akan kudin abinci da tafiye tafiye a 2019

Tabdijam! Buhari da Osinbajo zasu kashe N1.4bn akan kudin abinci da tafiye tafiye a 2019

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo zasu ci abinci na daruruwan miliyoyi tare da kasha wasu makudan miliyoyin wajen tafiye tafiye da yawon duniya, kamar yadda aka tanada musu a cikin kasafin kudin shekarar 2019.

Majiyar Legit.com ta ruwaito gwamnatin Najeriya ta ware kimanin naira biliyan daya da miliyan dari hudu da sittin da daya (N1,461,000,000) a kasafin kudin bana don kula da ire iren abinci, kayan kwadayi da ababen marmari da Buhari da Osinbajo zasu ci a shekarar 2019, da kuma tafiye tafiyensu da zasu yi.

KU KARANTA: Jiragen yakin Sojojin Najeriya sun yi ma yan bindiga ruwan azaba a Zamfara

Tabdijam! Buhari da Osinbajo zasu kashe N1.4bn akan kudin abinci da tafiye tafiye a 2019

Buhari da Osinbajo
Source: UGC

Daga cikin kudin N,461,000,000, an ware naira biliyan daya da miliyan daya da dubu dari uku da goma sha takwas da dari da saba’in da daya (N1,001,318,171) a matsayin kudin tafiye tafiyen Buhari a ciki da wajen kasar nan, sai kuma naira miliyan casa’in da takwas (N98,000,000) don ciyar da shi.

Yayin da aka ware naira miliyan dari uku da daya (N301,000,000) a matsayin kudin tafiye tafiyen mataimakin shugaba Osinbajo a ciki da wajen kasar nan, da kuma naira miliyan hamsin (N50,000,000) a kudin siyar da shi a shekarar 2019.

Bincike a kasafin kudin bana ya nuna an ware naira miliyan shida (N6,000,000) don sayen kwamfutoci da sauran kayan amfani a ofishin mataimakin shugaban kasa Osinbajo, sai kuma naira miliyan hudu (N4,000,000) don buga takardun aiki.

Sai dai idan aka kwatanta kasafin kudin shekarar 2019 da na shekarar 2017, za’a ga cewa adadin kudaden da aka ware ma tafiye tafiyen shugaban kasa mataimakinsa ya fi yawa a kasafin 2019 fiye da na 2017, amma kudin abinci ya ragu matuka a 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel