Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya

Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya

Babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kai ziyarar jaje ga babban hafsan rundunar Sojan sama, Iya mashal Saddique Abubakar inda ya jajanta masa bisa mutuwar wasu Sojoji guda biyar a Borno.

Wadannan Sojoji guda biyar sun fito ne daga rundunar Sojan sama, kuma sun mutu ne a yayin da suke fatawa da mayakan Boko Haram inda suke musu ruwan bama bamai, a haka ne jirginsu kirar Mi-35M ya samu matsala ya fado, babu wanda ya sha.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka wani babban jami’in karamar hukuma

Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya
Buratai da Sadique
Asali: Facebook

Sunayen wadanda suka mutu sun hada da Perowei Jacob, Kaltho Paul Kilyofas, Auwal Ibrahim, Adamu Nura da Meshack Ishmael, kuma lamarin ya faru ne a ranar Karaba 2 ga watan Janairu a daidai garin Damasak na jahar Borno.

A yayin ta’aziyyar daya kai, Buratai ya bayyana alhininsa bisa wannan babbar rashi, inda yace yana jajanta ma kafatanin dakaru da hafsoshin rundunar Sojan sama, iyalan mamatan da ma yan Najeriya gaba daya, sa’annan yayi fatan Allah Ya jikansu duka.

Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya
Buratai da Saddique
Asali: Facebook

Bugu da kari, Buratai yace ba zasu bari mutuwar Sojojin nan ta tafi a banza ba, zasu cigaba da jajircewa, dagewa tare da kara kaimi wajen yakin da suke da Boko Haram don ganin sun kawo karshen yan ta’adda da ayyukansu a yankin Arewa maso gabas da Najeriya gabaki daya.

Daga karshe ya umarci daraktan tattara bayanan sirri na rundunar Sojan kasa Manjo Jana SA Adebayo da kwamandan shiyya ta daya na Operation Lafiya Dole, Birgediya Bulama Biu su gabatar da addu’o’I don nema ma mamatan rahama.

Mutuwar Sojoji a jirgin sama: Buratai ya kai ma babban hafsan Sojan sama ziyarar ta’aziyya
Ziyarar
Asali: Facebook

A nasa jawabin, babban hafsan rundunar sojan sama, Saddique Abubakar ya gode ma Buratai da ma jami’an rundunar Sojan kasa gabaki dayansu bisa nuna damuwarsu da suka yi game da wannan rashi da suka yi, sa’annan ya dau alwashin zasu cigaba da aikinsu yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel