Mutuwar Shagari: Sarkin Kano, Ganduje da Tinubu sun kai ziyarar ta’aziyya Sakkwato

Mutuwar Shagari: Sarkin Kano, Ganduje da Tinubu sun kai ziyarar ta’aziyya Sakkwato

Tun bayan mutuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Usman Shehu Shagari a ranar Juma’a 28 ga watan Disamba ne jama’an Najeriya manya da kanana ke ta tururuwa zuwa gidansa dake babban birnin jahar Sakkwato don jajanta ma iyalansa tare da tayasu alhinin rashi.

A ranar 28 ga watan Disamba ne Alhaji Shehu Shagari tsohon shugaban kasa daga shekarar 1979 zuwa 1983 ya rasu a babban asibitin kasa dake Abuja inda yayi jinya bayan yayin fama da rashin lafiya, yana dan shekara 94 a rayuwa.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Gungun yan bindiga sun halaka wani babban jami’in karamar hukuma

Mutuwar Shagari: Sarkin Kano, Ganduje da Tinubu sun kai ziyarar ta’aziyya Sakkwato

Sarkin Kano
Source: Facebook

A ranar Alhamis 3 ga watan Janairu ne iyalan Shagari suka karbi bakoncin mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II tare da gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da jigon APC, kuma tsohon gwamnan jahar Legas, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu.

Haka zalika tsohon gwamnan jahar Adamawa Murtala Nyako na daga cikin wadanda suka kai ziyarar ta’aziya zuwa ga iyalan Shehu Shagari, shugaban jam’iyyar APC ta jahar Kano, Abdullahi Abbas, da fitaccen Malamin darika Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara.

Daga cikin wadanda suka fara kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan Shagari akwai shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya isa garin Sakkwato a ranar 30 ga watan Disamba, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Peter Obi da sauransu.

Mutuwar Shagari: Sarkin Kano, Ganduje da Tinubu sun kai ziyarar ta’aziyya Sakkwato

Nyako, Tinubu da Ganduje
Source: Facebook

Legit.com ta ruwaito a washegarin ranar da Buhari ya kai ziyarar jaje ga iyalan Shagari, tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya kai musu nasa ziyarar, shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai, gwamnan Borno Kashim Shettima.

Sauran sun hada da mataimakin gwamnan jahar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, gwamnan jahar Bauchi, Barista MA Abubakar, shugaban kungiyar Izala Sheikh Bala Lau, tare da sakataren kungiyar Sheikh Kabiru Gombe.

Anyi jana’izar marigayi Alhaji Usman Shehu Shagari a gidansa dake garin Shagari a ranar Asabar, inda aka kuma binneshi a cikin gidan, da fatan Allah Ya jikansa da gafara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel