Jiki magayi: Wata jami'ar Najeriya tayi watsi da ASUU, ta koma aiki
Wasu tsofin daliban jami'ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da yanzu ke koyarwa a jami'ar dake garin Ogbomoso, sun yi watsi da umarnin kungiyar malaman jami'o'i ta kasa (ASUU), sun koma bakin aiki a yau, Alhamis.
A jiya, Laraba, ne shugaban kungiyar ASUU reshen jami'ar, Dakta Abiodun Olaniran, ya fitar da sanarwar dake gargadi ga malaman jami'ar a kan komawa bakin aiki daga yau, Alhamis.
Dakta Olaniran ya kafe kan cewar jami'ar na cikin kungiyar ASUU, a saboda haka ba zata koma bakin aiki ba muddin ba uwar kungiya bata janye yajin aikin da ta shiga ba.
Sai dai a wata sanarwa da hukumar jami'ar ta fitar a yau, Alhamis, ta ce ba zata cigaba da yajin aikin ba tare da bawa malamanta umarnin su koma bakin aiki.
Kungiyar tsofin daliban makarantar sun bayyana cewar abun kunya ne jami'ar ta cigaba da yajin aiki bayan dawowar ta kwanan nan daga yajin aiki na tsawon shekaru biyu a kan matsalar karancin kudaden gudanarwa daga jihohin Oyo da Osun da suka mallaki jami'ar.
A sanarwa mai dauke da sa hannun Farfesa Omotayo Amuda da Dakta Azeem Ige, kungiyar tsofin daliban ta ce, "ba zamu zauna mu zuba ido da sunan biyayya ga ASUU ba ta hanyar cigaba da yajin aiki bayan shafe fiye da shekaru biyu muna yajin aiki yayin da ragowar jami'o'i ke aiki.
DUBA WANNAN: Zaben 2019: Ba zamu janye yajin aiki ba - ASUU
"Bayan doguwar mahawara tsananin kungiyar tsofin dalibai da hukumar makarantar, jami'ar LAUTECH na sanar da jama'a cewar ta koma bakin aiki daga yau, Alhamis, 3 ga watan Janairu, 2019."
Sai dai da majiyar mu ta tuntubi Olaniran ta wayar tarho, ya ce uwar kungiyar ASUU ce kadai keda ikon janye yajin aiki tare da bayyana cewar bashi da masaniyar komawar jami'ar LAUTECH bakin aiki.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng