Tsaro: An canja kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara

Tsaro: An canja kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara

An nada Zanna Mohammed Ibrahim a matsayin sabon kwamishinan rundunar 'yan sanda na jihar Zamfara da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Sanarwan nadin ya fito ne daga bakin mai magana da yawun hukumar, Muhammadu Shehu a ranar Alhamis 3 ga watan Janairun shekarar 2019.

Mr Ibrahim dan asalin jihar Borno ne kuma an haife shi ne a ranar 26 ga watan Nuwamban shekarar 1962. Ya yi digirinsa na farko da na biyu a Jami'ar Jos da ke jihar Plateau.

Mr Shehu ya ce sabon kwamishinan kwararen jami'in dan sanda ne.

Tsaro: An canja kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara

Tsaro: An canja kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara
Source: UGC

DUBA WANNAN: Wani uba ya bawa 'ya'yansa uku guba, da dalili

"Ya shiga aikin dan sanda ne a ranar 15 ga watan Mayun 1988," inji shi.

"Bayan kammala samun horo daga Police Academy da ke Kaduna, an aike da shi jihar Borno inda ya yi aikin shekara guda tare da hedkwatan 'yan sanda da ke Biu kuma daga baya ya yi aiki a wurare daban-daban," inji sanarwar.

"CP Zanna Mohammed Ibrahim Mni yana daya daga cikin mambobin kwamitin binciken satar man fetur da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya kafa a baya,

"A yayin da ya ke jawabi ga 'yan sandan jihar Zamfara, sabon kwamishinan ya jadda niyarsa ta inganta aikin samar da tsaro kamar yadda ya ke a tsarin Sufeta Janar na 'yan sanda, Ibrahim Idris."

Duk da karin jami'an 'yan sanda da sojoji da ake aikewa jihar ta Zamfara, 'yan bindiga na cigaba da kai hare-hare inda suka kashe mutane tare da bannata dukiyoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel