Ragon namiji: Yansanda sun yi ram da wani mutumi daya sumar da matar makwabcinsa, me yayi zafi?

Ragon namiji: Yansanda sun yi ram da wani mutumi daya sumar da matar makwabcinsa, me yayi zafi?

Rundunar Yansandan jahar Kaduna ta kama wani mutumi tare da makashi gaban kuliya manta sabo akan tuhumarsa da laifin lakada ma matar makwabcinsa dukan tsiya a dalilin wata yar sabanin fahim da suka samu a tsakaninsu.

Legit.com ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Barnawa ta jahar Kaduna, inda mutumin da ake tuhuma mai suna Gabriel Elijah dan shekara 35 ya lakada ma matar makwabcinsa Amaka Chinonso dukan tsiya.

KU KARANTA: Karancin albashi: Kungiyar kwadago zata cigaba da tattaunawa da gwamnati a ranar Juma’a

Sai dai bayan Yansanda sun samu nasarar kamashi, sun gurfanar da shi gaban kotun gargajiya dake unguwar Barnawa, inda suka tuhumarsa da laifin cin zarafin dan Adama tare da musguna masa, kamar yadda dansanda mai shigar da kara ya tabbatar.

Dansanda mai shigar da kara, Sajan Chidi Leo ya shaida ma kotun cewa Elijah ya aikata wannan laifi ne a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2018 a gidansa, inda yace bayan nan ne sai Amaka ta kai kararsa Caji ofis da nufin a bi mata hakkinta.

“Mutanen biyu sun samu matsalar fahimtar juna a tsakaninsu ne, daga nan ne Gabriel ya zage karfinsa ya casa Amaka, a dalilin dukan da yayi mata ta fadi sumammiya, duk da haka ya cigaba da dukanta, da kyar makwabta suka kwaceta daga hannunsa.” Inji shi.

A cewar Dansanda Leo, wannan laifi ya saba ma sashi na 240 na kundin hukunta laifuka, amma fa kiri da muzu Elijah ya musanta aikata wannan laifi a gaban kotu, hakan tasa Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel ya bada belinsa akan kudi N100,000, tare da mutane biyu da zasu tsaya masa.

Alkali Ibrahim ya bukaci mutanen biyu su kasance mazauna unguwar Barnawa, ya kasance suna da aikin yi, kuma suna da shaidar biyan kudaden haraji ga gwamnatin jahar Kaduna, daga nan y adage sauraron karar zuwa ranar 15 ga watan Janairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel