Fina-finan da su ka fi kowane armashi a shekarar da ta wuce a Kannywood
Yayin da aka ga karshen 2018, mun kawo jerun fina-finan da ake tunanin sun fi kowane sharara da ban-kaye a shekarar da ta gabata. Daga cikin fina-finan da su kayi tashe akwai Mariya, Ruwan dare, Li’ani da irin su fim din Takaddama.
Muhsin Ibrahim, wani Masani a harkar wasan kwaiwakyo da ke jami’ar Cologne ta kasar Jamus shi yayi nazarin wadannan fina-finai na bara.
Ga jerin nan kamar yadda BBC ta kawo su, sai dai ba a jeranta su bisa wata daraja ba.
1. Ruwan dare
Yaseen Auwalu ne yabada umarni a wannan fim da ya shahara. Wasu matasa ne su ka kamalla Digiri kuma su ka ce fau-fau ba za su yi wani aiki na gama-gari ba, illa aikin ofis mai tsokan gaske.
2. Mariya
A wannan shiri na Mariya, an ga yadda sha’anin auren dole yake a kasar Hausa. Wata yarinya ce mai suna Mariya aka yi aure da karfi da yaji duk da ta na da buri da kuma Masoyin ta dabam.
KU KARANTA: Jerin kyawawan ‘Yan matan da ake da su a gidan Kannywood
3. Rabiatu
Shi kuma wannan fim da Aminu Bono ya tsara, ya nuna matsalolin da ake fuskanta idan aka tura yarinya a matsayin ‘yar aikin gida. A wannan fim an rika takara wajen soyayya da wata mai aiki.
4. Fuska Biyu
Fim din Fusa biyu ya nuna matsalar yin aure a kasar Hausa ba tare da an yi wani kwakkwaran bincike ba. Akwai manyan ‘yan wasa irin su Adam Zango a wanan fim, inda ya fito da fuskoki biyu.
5. Kawayen Amarya
Yakubu Muhammad ne ya tsara shirin Kawayen Amarya inda aka ji labarin wani Attajiri mai mata 3 amma bai taba samun haihuwa ba. A karshe dai wata matar sa za ta samu juna-biyu a shirin.
Sauran fina-finan da su kayi fice a 2018 sun hada da, Li’ani, wanda aka tsara shi babu rawa da waka. Akwai fim din Risala na Sadiq S. Sadiq. Akwai kuma fina-finai irin su Hakki da Takaddama da kuma wani shiri mai ban-kaye mai suna Larai ko Jummai.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng