Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

A yayin da babban zaben shekarar 2019 ke kara katowa, yan siyasa daban daban da masu neman darewa madafan iko sun fara hada alaka da sashe na al’umma daban daban don cimma wannan buri nasu, tun daga matasa, dattawa, kungiyoyin mata, yan kasuwa da sauransu.

Sai dai da yake harkar fina finan Hausa na da matukar tasiri a yankin Arewacin Najeriya, hakan tasa masu shiryawa ko fitowa a cikin fina finan suka yi suna, tare da shahara ta hanyar daukakar da Allah yayi musu a wannan harka.

KU KARANTA: Kalli wasu mutane 4 da Ganduje zai nada mukaman Kwamishinoni a gwamnatinsa

Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

Kannywood
Source: Twitter

A sanadiyyar wannan daukaka da suka samu ne yasa yan siyasa ke gogoriyon janyosu a jiki domin shafan hasken taurarinsu, ta yadda zasu dinga gayyatarsu zuwa tarukan yakin neman zabensu, da kuma nema su buga musu wakoki da zasu kambamasu.

Shima a nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ba’a barshi a baya ba, inda uwargidarsa, Hajiya Aisha Buhari ta gayyato masa wasu fitattun jaruman Kannywood da zasu tallata shi tare da taya shi yakin neman zabe don cika burinsa na tazarce a zaben watan Feburairu.

Daga cikin wadannan shahararrun fuskokin da aka saba ganinsu a talabijin akwai;

Ali Nuhu

Adam A. Zango

Aminu Ala

Fati Abdullahi Washa

Halima Atete

Rukayya Dawaiyya

Maryam Yahaya

Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

Kannywood
Source: Twitter

Ali Isa Jita

Husainin Danko

Adamu Nagudu

Abubakar Sani

Jamila Nagudu

Fati Shi’uma

Hauwa Waraka

Shehu Hassan Kano

Ladidi Fagge

Suleiman Bosho

Dan Auta

Rabiu Rikadawa

Hajara Usman

Siyasar 2019: Fitattun jaruman Kannywood 20 da zasu yiwa Buhari yakin neman zabe

Kannywood
Source: Twitter

Sauran sun hada da Aminu Saira, Baban Chinedu, Yahaya Makaho, Sadi Sadi, Ado Gwanja, Fati Niger, Sadiq Mafia, Zuwaira Isma’il, Murja Baba, Hankaka, Sani Garba S.K, Ladidi Tubales, Haj Maryam CTV, Ibrahim Maishinku, Alhasan Kwalle, Rashida Adamu maisa’a, Bello Mohammed Bello, Sadiq Sani Sadiq, Naziru Ahmad da Falalu A Dorayi

Baya ga wadannan jarumai, akwai saura da dama, wadanda adadinsu ya haura mutane hamsin wadanda Aisha Buhari ta daukesu haya don ganin sun tallata hajar da maigidanta shugaba Buhari ya kasa a gabanin zaben 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel