2019: Farawa da iyawa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu karuwa

2019: Farawa da iyawa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu karuwa

Tsohon kaakakinmajalisar wakilan Najeriya, kuma gwamnan jahar Sakkwato Alhaji Aminu Wazirin Tambuwal ya shiga sabuwar shekarar 2019 da kafar dama, inda farawa da iyawa ya samu karuwa a iyalinsa.

Wannan karuwa da Gwamna Tambuwal ya samu shine haihuwa da Allah ya azurta matarsa, Hajiya Mairo Waziri Tambuwal da ita a ranar Laraba 2 ga watan Janairun 2019, inda Allah ya azurtasu da samun diya mace.

KU KARANTA: Kalli wasu mutane 4 da Ganduje zai nada mukaman Kwamishinoni a gwamnatinsa

2019: Farawa da iyawa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu karuwa

Tambuwal ya samu karuwa
Source: Facebook

Idan za’a tuna a ranar 4 ga watan Feburairu na shekarar 2016 ne Gwamna Tambuwal ya auri Hajiya MaryamMairo Mustapha a matsayin sabuwar matarsa, inda aka sha shagalin bikin a jahar Kano, kamar yadda Legit.com ta ruwaito.

A lokacin da aka yi bikin aurenta da Tambuwal, Maryam tana yar shekara Talatin da shida ne a rayuwa, kuma mahaifinta tsohon dan siyasan jamhuriya ta biyu ne, haka zalika tayi karatun sakandari a makarantar mata ta gwamnatin tarayya dake Kazaure, sai kuma karatun digiri a jami’ar Bayero ta Kano.

Wannan haihuwa da matar Tambuwal ta yi ya kawo adadin yayansa zuwa biyar kenan, biyu dsaga cikinsu maza, sai kuma sauran ukun mata, amma sauran yayan nasa guda hudu yaya ne ga uwargidarsa Mariya.

2019: Farawa da iyawa, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya samu karuwa

Jaririyar
Source: Facebook

A wani labarin kuma Gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya amince da nadin Mai Sharia Alkali Saidu Sifawa a matsayin sabon mukaddashin babban alkalin jahar Sakkwato, watau Alkalin Alkalan jahar Sakkwato.

Draktan watsa labaru na fadar gwamnatin jahar Sakkwato, Malam Abubakar Shekara ne ya sanar da sunan Saidu Sifawa a matsayin sabon mukaddashin Alkalin Alkalan jahar, inda yace nadin ya fara ne daga ranar 31 ga watan Disamba.

Darakta Shekara yace gwamnan ya nada Sifawa ne biyo bayan murabus tare da ajiye aiki da tsohon Alkalin Alkalan jahar, Mai Sharia Bello Abass yayi sakamakon cika shekaru sittin da biyar a rayuwa da yayi, haka zalika Mai Sharia Bello Duduwale ya ki amincewa a nada shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel