Na keta haddin Baiwar gidan mu a lokacin samartaka - Shugaban Kasar Philippine

Na keta haddin Baiwar gidan mu a lokacin samartaka - Shugaban Kasar Philippine

Za ku ji cewa, shugaban kasar Phillipine, Rodrigo Duterte, ya yi ikirari tare da furucin yadda ya keta haddin wata Baiwar gidan su a sa'ilin da ya ke samartaka kamar yadda rahotanni da sanadin jaridar The Punch suka bayyana.

Yayin gabatar da jawabansa a ranar 29 ga watan Dasumba na shekarar da ta gabata, Duterte ya yi ikirarin fallasa kan sa gaban wani Malamin Addini, inda ya zayyana ma sa yadda ya rika cin zarafin wata Baiwar gidan su a lokacin kuruciya da kuma samartaka.

Rahoton da mujallar Times Magazine ta tsakuro daga kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa, Duterte ya yi ikirarin yadda kuruciya ta rude sa ya rika burmawa dakin Baiwar gidansu yana lalube ma ta 'yan matancin ta da yatsunsa na hannu a yayin da take bacci.

Rodrigo Duterte

Rodrigo Duterte
Source: UGC

Sai dai rahoton wannan lamari bai kasance abun ban mamaki ba ga al'ummar kasar sa sakamakon yadda ya kasance akan ganiyarsa ta da'awar cin zarafi da keta haddin Mata da ta janyo ma sa abun Allah wadai gami da suka a kasar.

KARANTA KUMA: Hukumar sojin sama ta tarwatsa sansanin Boko Haram a garin Baga

A watan Yuni da kuma Yuli na shekarar da ta gabata, wata kungiyar kare martabar Mata ta yi dandazo a garin Manila dangane da yadda shugaban kasa Duterte ya yi da'awar a rika harbin Mata 'yan tawayen gurguzu a 'yan Matancin su.

Duterte ya kara da cewa, bayan zayyanawa babban Malamin laifin da ya aikata lokacin sa na samartaka, babban Malamin ya yi masa albishir na bakin goro da cewa ba bu shi ba bu rabauta domin kuwa ya yi hannun riga da rahamar Mahaliccin sa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel