Rugujewar gini: Allah Ya yi ma wani jariri gyadar doguwa bayan kwashe awanni 35 cikin baraguzai
Kamar yadda bahaushe ke fade “Ka gode ma Allah ko kana bakin kura ne” tunda dai bata cinyeka ba akwai yiwuwar ka kubuta, hakan ne ta tabbata da wani dan jaririn yaro wanda baraguzan gini suka danneshi a kasar Rasha na tsawon awanni Talatin da biyar, amma ya rayu.
Majiyar Legit.com ta ruwaito ginin da aka tsinci jaririn ya rushe ne bayan fashewar wata na’urar iskar gas, wanda ta rusa dakuna arba’in da takwas dake wani gida mai hawa goma a birnin Magnitogorsk na kasar Rasha.
KU KARANTA: Yan kasuwa sun tafka mummunan asara a wata gobara da ta tashi a kasuwan Kaduna
Rahotanni sun ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Litinin 31 ga watan Disambar shekarar 2018, inda yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane bakwai, tare da jikkata wasu da dama, har yanzu kuma ba’a gano inda mutane Talatin da shida suka shige ba.
Sai dai duk wannan bala’I daya faru, Allah ya tseratar da jaririn a can kasan baraguzan ginin, kuma ga tsananin sanyi da ake bugawa a kasar, hakan ne yasa ma’aikatan bada agajin gaggawa suka bayyana lamarin a matsayin baiwa.
Wani bidiyo daya watsu a kafafen sadarwar zamani kamar yadda jami’an hukumar bada agajin gaggawa suka dauka ya nuna wani jami’in hukumar ya kwakulo jaririn daga cikin baraguzan yana sanye da safa, sa’annan ya lullubeshi da bargo, inda ya nufi motar bada agaji da gudu.
Wani jami’in hukumar ya bayyana cewa sun jiyo kukan jaririn ne daga kasa, toh amma saboda yanayi irin na baraguzan ginin zasu iya ruftawa, hakan yasa ake tsoron shiga cikinsu, amma saboda wannan jariri aka shirya wani aikin ceton rain a musamman.
“Daruruwan jama’a suna ta tsumayin ganin an ceto wannan jariri dan baiwa, kuma mun samu nasarar zakulosa daga cikin baraguzan, abin yazo da mamaki da tausayi matuka, hatta jami’anmu sai da suka zubar da hawaye don murna da tausayi.” Inji jami’in hukumar.
Sai dai koda aka garzaya da shi zuwa Asibiti domin samun kulawa, likitoci sun bayyana cewa yana dauke da ciwo a cikin kansa sakamakon buguwa da yayi, amma yana samun sauki, kuma mahaifiyarsa na nan da ranta, ita ke jinyarsa a asibiti.
Shima ministan lafiya na kasar Rasha, Veronika Skvortsova ta bayyana farin cikinta da yadda ake ceto jaririn, haka zalika ta bayyana alhininta ga wadanda lamarin ya shafa, amma tace alamu sun nuna ba lallai a sake gano wani mazaunin gidan da rai ba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng