Duniya mai yayi: Alkalin Alkalai na jahar Sakkwato ya yi murabus

Duniya mai yayi: Alkalin Alkalai na jahar Sakkwato ya yi murabus

Babban alkali kuma alkalin alkalan jahar Sakkwato, Mai sharia Bello Abass yayi murabus daga aiki bayan cimma wa’adin ajiye aiki kamar yadda dokokin aikin gwamnati ta tanadar, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito gwamnan jahar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ya tabbatar da amincin Abass a matsayinsa na Alkali mai gaskiya da adalci, Tambuwal ya bayyana haka ne a yayin bikin da aka shirya ma Alkalin na barin aiki.

KU KARANTA: hausa.legit.ng/1212818-gagarumin-yajin-aiki-zamu-gwabza-da-gwamnati-akan-karancin-albashin-n30-000.html

Duniya mai yayi: Alkalin Alkalai na jahar Sakkwato ya yi murabus

Abass da Tambuwa
Source: Twitter

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya nada Abass mukamin Alkalin Alkalan jahar Sakkwato ne a shekarar 2016 bayan tsohuwar Alkalin Alkalai Aisha Dahiru ta yi murabus, inda a yanzu ya ajiye aiki bayan cimma wa’adin cika shekaru sittin da biyar a rayuwa.

Gwamna Tambuwal ya samu wakilcin sakataren gwamnatin jahar Sakkwato, Farfesa Bashir Garba ne a yayin wannan biki, wanda ya bayyana Alkali Abass a matsayin mutum mai tsantsani, sanin ya kamata da kuma kwararre a sha’anin sharia.

Shima kwamishinan sharia na jahar Sakkwato, kuma babban lauyan gwamnati, Barista Sulaiman usman ya jinjina ma Alkali Abass tare da yabawa da rawar daya taka a sha’anin sharia a zamanin da yake aiki ta hanyar gaggauta yanke hukuncin adalci.

Bugu da kari, tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen Arewa maso yamma, kuma tsohon ministan wasanni a zamanin mulkin shugaba Goodluck Jonathan, Inuwa Abdulkadir ya bayyana Alkalin a matsayin abin koyi ga sauran Alkalai, musamman masu tasowa.

Da yake nasa jawabi, Alkali Abass ya bayyana godiyarsa ga dukkanin mutanen da yayi aiki dasu wadanda suka basi gudunmuwa a aikinsa, musamman gwamnan jahar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya bayyana shi a matsayin ginshikin samun nasararorin da yayi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel