Sai da Shagari ya yafewa kowa kafin ya bar Duniya – Bala Shagari

Sai da Shagari ya yafewa kowa kafin ya bar Duniya – Bala Shagari

Babban ‘Dan marigayi Alhaji Shehu Shagari watau Bala Shagari ya bayyana yadda Mahaifin sa ya komawa Ubangijin sa. Bala Shagari yace tsohon shugaban kasar bai bar Duniya yana rike da wani ta’aliki ba.

Sai da Shagari ya yafewa kowa kafin ya bar Duniya – Bala Shagari

Shehu Shagari bai bar Duniya da fushin wani mutumi ba
Source: UGC

Bala Shagari yace sai da Mahaifin na sa mai shekaru fiye da 90 ya yafewa kowa a Duniya kafin ya cika. Shagari yayi wannan jawabi ne domin fayyace gaskiyar maganar da ke yawo na cewa Shehu Shagari yana fushi da wasu Bayin Allah.

Alhaji Bala Shagari yace ba gaskiya bane da ake cewa Dattijon ya rasu yana jin haushi wasu, Bala yace sai da Marigayin ya yafewa duk wadanda su kayi masa laifi a baya. Ya kuma kara da cewa rashin lafiya ce ta rike hana Dattijon ya rika fita.

KU KARANTA: Sanatan Arewa ya bayyana inda Shagari ya sha ban-ban da sauran shugabanni

Bala yayi hira da ‘Yan jarida bayan rasuwar tsohon shugaban kasar a Sokoto inda ya bayyana cewa Shehu Shagari ya dauki tsawon lokaci ba ya iya zuwa ko ina saboda larurar rashin lafiya. Shehu Shagari ya rasu ne ya ba shekaru 93 baya a Duniya.

A jiya ne dai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taka har Sokoto inda yayi wa Iyalin Marigayin ta’aziyya tare da alkawarin tunawa da tsohon shugaban kasar. Shugaban kasar bai iya halartar jana’izar Shagari ba sai dai ya aiko babban wakili.

A rana irin ta yau ne sojoji su ka kifar da gwamnatin Shagari a shekarar 1983 inda Janar Muhammadu Buhari ya dare kan mulki. Iyalin tsohon shugaban kasar dai sun bayyana cewa Marigayin bai mutu yana jin haushin kowa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel