Akwa Ibom: Shugaba Buhari zai samu gagarumar nasara a zaben 2019 – Inji Ambode

Akwa Ibom: Shugaba Buhari zai samu gagarumar nasara a zaben 2019 – Inji Ambode

- Akinwunmi Ambode ya yabawa mutanen Akwa Ibom da su ka tarbi Buhari

- Gwamnan yace taron jama’an da ya gani ya nuna Buhari zai yi nasara a 2019

- Ambode yace idan Buhari ya zarce za a samu cigaba da fuskar tattali da tsaro

Akwa Ibom: Shugaba Buhari zai samu gagarumar nasara a zaben 2019 – Inji Ambode

Gwamnan Legas yace Buhari ya ci zabe ya gama a 2019
Source: Twitter

Kwanan nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman zaben sa a Garin Uyo da ke Jihar Akwa-Ibom. Jama’a da dama sun fito sun tarbi shgaban kasar a wani filin wasan kwallon kafa da ke babban birnin Uyo.

Gwamna Akinwunmi Ambode yayi magana game da zaben 2019, inda yace irin dubban jama’an da ya gani wajen yakin neman zaben na APC ya tabbatar masa cewa shugaba Buhari ne zai sake lashe zaben da za ayi a farkon badi.

Gwamnan na Legas ya fadawa ‘yan jarida a Garin na Uyo cewa babu tababa lallai Buhari zai yi nasara a 2019. Ambode yace idan har dubban mutane za su fito wajen kamfen din Buhari, hakan na nuna cewa shugaban kasar zai zarce.

KU KARANTA: Jonathan ya maidawa ‘Dan takarar Mataimakin Gwamna a APC a Legas martani

Habib Aruna wanda shi ne ke magana da yawun bakin gwamnan na APC ya fitar da jawabi, inda yace mutanen kudu maso kudu sun fara yin amanna da tafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma mataimakin sa, Yemi Osinbajo.

Ambode yace idan Buhari ya samu zarcewa a kan karagar mulki, za a ga cigaba wajen gine-ginen abubuwa more rayuwa da kuma fuskar tattalin ariki da sha’anin tsaro. Gwamnan yace APC tayi abin da ya taba al’umma a cikin shekaru 3

Gwamnan na Legas wanda ba zai koma kan kujerar sa ba, ya bayyana cewa zaben Muhammadu Buhari da Farfesa Yemi Osinbajo a jam’iyyar APC a 2019 shi ne kurum mafita domin a cigaba da gyara kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel