Zargin cin hanci: Obafemi Hamzat kasurgumin makaryaci ne inji Goodluck Jonathan

Zargin cin hanci: Obafemi Hamzat kasurgumin makaryaci ne inji Goodluck Jonathan

- Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karyata zargin Obafemi Hamzat

- Obafemi Hamzat yayi ikirarin Jonathan ya sa sa cin hanci a lokacin zaben 2015

- Jonathan ya maidawa Hamza martani ne ta bakin wani mai magana da yawun sa

Zargin cin hanci: Obafemi Hamzat kasurgumin makaryaci ne inji Goodluck Jonathan
Jonathan ya karyata zargin bada makudan Daloli domin doke Buhari a 2015
Asali: Depositphotos

‘Dan takaran mataimakin gwamnan jihar Legas a jam’iyyar APC, Dr Obafemi Hamzat, yayi ikirarin cewa tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan ya ba sa cin hancin kudi har Dala miliyan 5 a sa’ilin da yake neman zabe a 2015.

Goodluck Jonathan yayi maza ya karyata wannan magana a wani jawabi ta hannun mai magana da yawun sa watau Ikechukwu Eze. Tsohon shugaban kasar yace bai taba haduwa da Obafemi Hamzat a lokacin yakin zaben 2015 ba.

Tsohon shugaban kasar yace babu alamun gaskiya ko kusa-ko a nesa a jawabin ‘dan takaran na APC. Jonathan yace Hamzat yana neman kuri’un jama’a ne a 2019 ido rufe don haka yake sakin baki yana fadar duk abin da za ya zo masa.

KU KARANTA: Zaben 2019: PDP za ta ba Buhari mamaki a Jihar Filato - Sen. Useini

Hadimin tsohon shugaban kasar yace a lokacin da ake yakin neman zabe a 2015, babu wanda ya san wani ‘Dan siyasa mai kama da Obafemi Hamzat don haka babu dalilin da zai sa Goodluck Jonathan ya gana da shi har ya ba shi cin hanci.

Bayan nan kuma dai Dr. Jonathan ya tunawa jama’a cewa bai yi imani da siyasar a-mutu ko –yi-rai ba don haka babu dalilin da zai sa ya bada kudi domin ganin ya ci zabe. Jonathan yace maganar cewa ya bada cin hancin Dala miliyan 5 karya ne.

Jonathan yace abin kunya ne ace wanda yake neman kujerar gwamna a daya daga cikin jihohin Najeriya ya buge da sheka karya babu kunya kuma babu tsoron Allah. Jonathan ya nemi Hamzat ya fadi wadanda su ka ba shi kudi da kuma shaidar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel