Kan mu daya da Atiku wajen ganin mun yi waje da APC – ‘Dan takaran Gwamnan Filato

Kan mu daya da Atiku wajen ganin mun yi waje da APC – ‘Dan takaran Gwamnan Filato

Mun ji cewa ‘Dan takaran gwamnan jihar Filato a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Laftana Janar Jeremiah Useni mai ritaya ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta ga abin ban mamaki a zaben da za ayi a 2019.

Kan mu daya da Atiku wajen ganin mun yi waje da APC – ‘Dan takaran Gwamnan Filato

PDP za ta hada kai domin tika Buhari da kasa a Filato inji Useini
Source: UGC

Janar Jeremiah Useni ya bayyana wannan ne lokacin da ya gana da ‘yan takaran PDP na kujeran majalisar wakilai da kuma sanatoci a zaben 2019. An yi wannan ganawa ne a sakatariyar jam’iyyar da ke cikin garin Jos a jihar Filato.

Useini ta tabbatar da cewa a shirya yake ya fitar da mutanen Filato daga halin kangin da su ka shiga a wannan gwamnatin. Useini ya kuma sha alwashin yin aiki tare da Atiku Abubakar domin ganin PDP tayi nasara a zaben badi.

KU KARANTA: Ministan Buhari da ke Filato ya halarci bikin gargajiya da bante

Janar Useini yayi karin haske game da rade-radin da ke yawo na cewa ba ya tare da ‘dan takaran PDP na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar. Useini yace babu wani rabuwar kai tsakanin sa da Atiku kamar yadda wasu ke ta yadawa.

‘Dan takaran na PDP yace zai cigaba da ganawa da masu harin kujeru a zaben 2019 a karkashin jam'yyar, yana kuma mai sa rai cewa za su yi nasara a zabukan shugaban kasa da gwamna da kuma ‘yan majalisun jiha da na tarayya.

Shugaban PDP na Filato, kuma tsohon ministan matasa da wasanni a Najeriya, Damishi Sango, ya koka da yadda masu rike da madafan iko a Filato ke hana su lika allon kamfe a wasu manyan wurare a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel