Dalilin cire Aliko Dangote daga cikin kwamitin yakin neman zaben Buhari

Dalilin cire Aliko Dangote daga cikin kwamitin yakin neman zaben Buhari

Mun samu labarin dalilin da ya sa fadar shugaban kasa tayi maza ta cire sunan Attajirin Afrika watau Aliko Dangote daga cikin kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari daga bakin jam’iyyar hamayya.

Dalilin cire Aliko Dangote daga cikin kwamitin yakin neman zaben Buhari
Da alama Aliko Dangote ba zai so yayi aiki da APC a 2019 ba
Asali: UGC

Rahotanni sun zo mana cewa an cire Aliko Dangote daga cikin wadanda za su taimaka wajen ganin shugaba Muhammadu Buhari ya zarce a kan karagar mulki a 2019 ne bayan Attajirin ya nuna cewa bai ji dadin jefa sa cikin kwamitin ba.

Wani babban ‘Dan adawa a Najeriya daga jam’iyyar hamayya ta PDP ya bayyana mana cewa Alhaji Aliko Dangote ya nuna fushin sa bayan ya ji ana neman a kakaba sunan sa cikin masu taya Muhammadu Buhari yakin tazarce a zaben 2019.

KU KARANTA: Dangote bai cikin kungiyar yakin zaben Buhari - Fadar shugaban kasa

A cewar wannan ‘Dan siyasa da aka sakaya sunan sa, Aliko Dangote wanda ya fi kowa kudi a Najeriya da ma kaf Afrika yayi kokarin nunawa APC cewa ba ya bukatar su cusa shi cikin wadanda za su taya jam’iyyar neman takara a zabe mai zuwa.

'Dan siyasan yace, jam’iyyar ta APC mai mulki tana shure-shuren mutuwa ne domin kuwa ta rasa duk wani farin jini da kima a idanun mutanen Najeriya. ‘Dan siyasar ya nemi jam’iyyar su daina karya da yaudarra jama’a su nemi afuwar jama’a.

Wannan labari dai bai shiga hannun ‘yan jarida ba a yanzu haka. Wanda ya bayyana wannan din yayi hakan ne a cikin wata hira da aka yi da shi a wata ganawa da bai san ‘yan jarida su na kusa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel