Rikicin Zamfara: Dakarun Sojojin saman Najeriya sun fatattaki ‘Yan ta’adda

Rikicin Zamfara: Dakarun Sojojin saman Najeriya sun fatattaki ‘Yan ta’adda

Sojojin sama na Najeriya sun rutsa wasu daga cikin tsagerun da su ka fitini jama’a a Yankin Jihar Zamfara. Wani babban jami’i na sojojin saman kasar ya bayyana mana wannan a shafin sa na Facebook.

Rikicin Zamfara: Dakarun Sojojin saman Najeriya sun fatattaki ‘Yan ta’adda
Dakarun Operation DIRAN MIKIYA sun shiga cikin Zamfara
Asali: Twitter

Rundunar sojojin sama na kasar nan na Operation DIRAN MIKIYA, sun dura cikin wani kauye da ake kira Tsamari a cikin Garin Birnin Magaji a Jihar Zamfara. Sojojin sun fatattaki tsagerun da ke haddasa fitina a wannan gari.

Sojojin na Operation DIRAN MIKAYA sun shiga wannan daji ne a ranar juma’a da sassafe, bayan sun samu labarin cewa tsagerun da ke kashe jama’a a Yankin su na boye a cikin wannan daji. Wannan ya sa ‘yan iskan su ka tsere.

KU KARANTA: Boko Haram: Sojoji na shirin yiwa mutanen Baga canjin matsuguni

Kamar yadda sojojin saman kasar su ka bayyana, an aika da jirgin Alpha Jet wanda ya rika sintiti a inda ‘yan iskan su ke boye. Sojojin sun yi nasarar yin kaca-kaca da mafakar 'yan ta’addan tare da fatattakar su daga cikin dajin.

Haka-zalika, an kuma samu kayan aiki da kuma babur daga dajin bayan ‘yan ta’addan sun tsere. Yanzu haka sojojin na sama su na cigaba da laluben ‘yan ta’adda a Yankin domin ganin an kawo karshen kashe-kashen da ake yi.

Ibekunle Daramola, wanda shi ne babban jami’in yada labarai sojojin saman Najeriyan ya bayyanawa jama’a cewa za su cigaba da aika Runduna ta musamman domin ganin an kawo zaman lafiya a cikin Arewa maso yammacin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel