EPL: Labarin wasannin Gasar Firimiya na wannan makon

EPL: Labarin wasannin Gasar Firimiya na wannan makon

A wannan karo, mun leka harkar wasanni inda mu ka kawo maku labarin gasar Firimiya na Ingila na wannan makon. A jiya Asabar an buga wasanni 5. Babban wasan da aka buga shi ne tsakanin kungiyar Arsenal da Liverpool.

EPL: Labarin wasannin Gasar Firimiya na wannan makon
Firiminho ya jefawa Arsenal kwallaye 3 a wasan jiya
Asali: Getty Images

1. Watford v Newcastle

An yi kunnen doki a wasan Watford da kuma kungiyar Newcasle jiya. Solomon Randon ne ya ci wa Newcastle kwallo a minti na 25 kafin Abdolaye Doucore ya rama daf da a tashi wasan.

2. Brighton v Everton

J. Locadia ne ya ci wa Brighton wani kwallo da ya makalewa Everton a wuya a wasan su na jiya. Yanzu dai Everton ta na matsayi na 10 a teburin firimiya, yayin da Brighton ta ke na 13 a tebur.

KU KARANTA: Zidane zai nemi ya maye gurbin Jose Mourinho a Manchester

3. Tottenham v Wolves

Wani wasa da ya ba mutane mamaki shi ne wasan Tottenham da kuma Wolves a gidan Tottenham. Harry Kane ne ya ci mai ‘ya ‘ya a minti na 22. An dirkawa Tottenham din kwalla 3 daga baya.

4. Fulham v Huddersfield

Huddersfield ta kara shan kashi a wannan makon a hannun kungiyar Fulham. Alex Miltrovic ya ci kwallo a minti na 90+1 yayin da ake shirin busa tashi. Huddersfield ce ta karshe a tebur har yanzu.

5. Arsenal v Liverpool

Kungiyar Arsenal ba ta ji dadi a filin wasa na Anfield ba jiya. Arsenal ta ci kwallo mai ‘ya ‘ya bayan da Liverpool ta jibga mata ci 5 ya hannun Salah da Mane da Firiminho wanda ya ci 3.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel