Shugaban kasa Buhari ya ki zuwa sallar jana’izar Shagari
A Ranar Juma’a ne aka ji wani labari mai matukar ban takaici na rasuwar tsohon shugaban Alhaji Shehu Shagari. An binze Shehu Shagari ne a Jihar Sokoto a Ranar Asabar bayan ya rasu a yammacin Ranar Juma’a.
Jama’a da dama sun hallara wajen yi wa tsohon shugaban kasar na Najeriya sallar jana'iza. Sai dai shugaban kasa Muhammadu Buhari bai halarci taron jana’izar da aka yi a Garin na Sokoto ba. Shugaba Buhari ya aika wakili ne zuwa wurin.
Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari da mukarraban gwamnatin sa a wajen sallar da aka yi Shehu Shagari. Ko da dai Sakataren gwamnatin na Najeriya ba musulmi bane.
KU KARANTA: Buhari ya ba da umarnin nade tuta na tsawon kwana uku saboda rasuwar Shagari
Wadanda su ka halarci jana’izar marigayin sun hada da gwamnoni irin su Rt. Hon.Aminu Waziri Tambuwal, Abdulaziz Yari, da Sen. Atiku Bagudu na jihohin Arewa da kuma tsohon gwamnan Sokoto, Attahiru Bafarawa da mutane da-dama.
Buhari ne dai ya hambarar da Shagari a Disamban 1983. Daga cikin Iyalin Marigayin akwai tsohon ministan ruwa na Najeriya a lokacin gwamnatin Obasanjo watau Muktar Shehu Shagari. Shehu Shagari ya bar Duniya ne yana da shekaru 93.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa za a sauke tutar Najeriya na kwana 3 domin jimamin rashin tsohon shugaban kasar. Tuni dai Shugaba Buhari ya aika ta'aziyyar sa ga mutanen Najeriya game da wannan babban rashi da aka yi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng