Mutuwar Shagari: Buhari ya bayar da umarnin nade tuta na tsawon kwana uku

Mutuwar Shagari: Buhari ya bayar da umarnin nade tuta na tsawon kwana uku

A sakonsa na ta'aziyya, shugaba Buhari ya bayar da umarnin a sauke tutar Najeriya daga kololuwar karfe zuwa tsakiya har na tsawon kwanaki domin nuna alhinin rashin tsohon shugaban kasa marigayi Shagari.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sakonsa na ta'aziyya bisa rashin tsohon shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari, da Allah ya yiwa rasuwa a jiya, Juma'a.

Wannnan umarnin na shugaban kasa ya fi shafar barikin sojoji da na ragowar jami'an tsaro da kuma ragowar ma'aikatu da hukumomi na gwamnatin tarayya.

A sakon da ya sanya wa hannu da kansa, Buhari ya bayyana cewar tuni shi da Shagari suka fahimci juna duk da kasancewar akwai sabani a tsakaninsu a baya.

"Marigayi Shagari ya kasance mutum mai bangare da yawa: malamin makaranta, dan siyasa, ma'aikacin gwamnati, minista, sannan shugaban kasa. Ya yiwa Najeriya hidima tukuru.

Mutuwar Shagari: Buhari ya bayar da umarnin nade tuta na tsawon kwana uku
Marigayi Alhaji Shehu Shagari
Asali: Facebook

"Amadadina da iyalina da gwamnatin tarayya, ina mika sakon ta'aziyya ga dukkan 'yan Najeriya, musamman iyalin marigayin da gwamnatin Sokoto da jama'ar jihar, bisa rashin da muka yi. Ina yi masa fatan samun rahama," a sakon Buhari.

A yau, Asabar, ne aka binne gawar tsohon shugaban kasar Najeriya na farko a mulkin dimokradiyya, Marigayi Alhaji Shehu Shagari, a mahaifar sa, karamar hukumar Shagari, dake jihar Sokoto.

Tsohon shugaban jami'ar Usman Danfodio Sokoto, Farfesa Shehu Galadanchi, ne ya jagoranci sallar jana'izar tsohon shugaban kasar da misalin karfe 3:30 na rana.

DUBA WANNAN: 2019: Tsohon janar a rundunar soji ya shawarci masu takara da Buhari

Tun da farko, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tare da manyan jami'an gwamnatinsa sun tarbi gawar tsohon shugaban kasar a filin tashi da saukar jiragen sama na Sultan Abubakar dake garin Sokoto.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci jana'izar marigayi Shagari akwai sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara.

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega, tsohon minsta, Mukhtar Shagari, Sanata Aliyu Magatakarda Wamako, da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel