APC ba ta da shirin mika mulki ga kabilar ibo - Obasanjo

APC ba ta da shirin mika mulki ga kabilar ibo - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya gargadi 'yan kabilar Igbo suyi takatsantsan da alkawurran da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ke musu gabanin babban zaben 2019.

Obasanjo ya yi wannan gargadin ne a ranar Asabar a wurin taron masu ruwa da tsaki a garin Ukpor, a karamar hukumar Nnewi ta Kudu a garin Anambra inda ya ce APC ba ta da niyyar mika shugabanci ga kabilar Igbo.

Ya yi kira ga 'yan kabilar Igbo su hada kansu wuri guda saboda suyi tasiri a babban zaben shekarar 2019.

APC ba ta da shirin bawa Igbo shugabancin kasa - Obasanjo

APC ba ta da shirin bawa Igbo shugabancin kasa - Obasanjo
Source: UGC

Ya ce, "Ina kira gare ku da kada ku amince wani ya mayar da ku baya saboda kuna da matukar muhimmanci a kasar nan.

"Babban hatsari ne amincewa da gwamnatin APC," inji Obasanjo.

DUBA WANNAN: Buhari ya raba gardama a jihar Ogun: Ya zabi daya daga cikin 'yan takarar APC

Bayan ya yabawa Peter Obi, Obasanjo ya shawarce shi ya hada gwiwa da masu ruwa da tsaki a yankin Kudu maso gabas domin neman kuri'un al'umma a zaben shugabancin kasa na shekarar 2019.

"Kai da dan takarar shugabancin kasa na PDP kuna 'yan Najeriya da suka kwashe shekaru hudu suke sa ran za ku cece su.

"Dole sai kunyi tunanin yadda za ku ceto kasar nan daga halin da gwamnati mai ci yanzu ta jefa kasar.

"Duba da gogewa da ka samu a matsayinka na gwamna, ina sa ran za ku dai-daita al'umurra Najeriya a matsayinka na mataimakin shugaban kasa," inji Obasanjo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel