Cikin a gaggawa: An tsige shugabanni hudu a majalisar dokokin jihar Adamawa

Cikin a gaggawa: An tsige shugabanni hudu a majalisar dokokin jihar Adamawa

A wani zama na musamman da majalisar dokokin jihar Adamawa tayi a yau, Asabar, mambobin majalisar sun tsige Emmanuel Tsamdu, mataimakin kakakin majalisar jihar, da Hassan Barguma, shugaban masu rinjaye.

Kazalika majalisar ta tsige mataimakin shugaban masu rinjaye, Abubakar Isa, da mataimakin bulaliyar Abdullahi Nyapak.

Majalisar ta amince da nadin Lumsabani Dilli a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar da kuma nadin Hayatu Atiku a matsayin shugaban masu rinjaye.

Safiyanu Aminu Aliyu (mai wakiltar mazabar Song) ya zama sabon mataimakin bulaliyar majalisar, yayin da Sani Shehu (mai wakiltar mazabar Mubi) ya zama mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Cikin a gaggawa: An tsige shugabanni hudu a majalisar dokokin jihar Adamawa

Majalisar dokokin jihar Adamawa
Source: Twitter

Shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa, Alhaji Kabiru Mijinyawa, ya tabbatar da faruwar tsige shugabannin majalisar da kuma nadin wasu sabbi, sai dai a a nasa martanin, Emmanuel Tsamdu, ya yi watsi da batun tsige shi, yana mai bayyana cewar, "mutane 13 ba zasu iya tsige ni daga mukamina ba."

Majalisar dokokin jihar Adamawa na da mambobi 25.

Sai dai har yanzu majalisar bata bayyana dalilin daukan wannan mataki ba.

DUBA WANNAN: An binne marigayi tsohon shugaban kasa Shagari a mahaifar sa, hotuna

Tsohon gwamnan jihar Legas a mulkin soji, Burgideya janar Buba Marwa, ya ce babu gurbin zama shugaban kasa ga kowanne mutum bayan shugaba Buhari a shekarar 2019.

Marwa, shugaban kwamitin da zai bawa shugaban kasa shawara a kan dakile shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa, ya fadi hakan ne yayin amsa tambayoyin 'yan jaridu a garin Yola, jihar Adamawa.

Marwa ya ce ba ya shakkar cewar shugaba Buhari zai sake lashe zabe a shekarar 2019.

"Kungiyar Buba Marwa ce ta fara shirya taron gangamin goyon bayan shugaba Buhari a 2016 domin yin godiya da nuna jin dadi bisa yadda shugaba Buhari ya yi kokari a bangaren inganta tattalin arziki, inganta tsaro da yaki da cin hanci.

"Zai kara lashe zabe a shekarar 2019 da yardar Allah," a kalaman Marwa.

Da yake magana a kan batun tsaro, Marwa ya jinjinawa sojojin Najeriya tare da yin kiran ga 'yan Najeriya da su goyon baya domin samun nasara a aiyukan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel