Kiwon Lafiya: Nau'o'in abinci 5 da za su kare ka daga kamuwa da mura

Kiwon Lafiya: Nau'o'in abinci 5 da za su kare ka daga kamuwa da mura

A lokacin hunturu mutane sun fi kamuwa da mura, tari da sauran matsalolin da suka shafi huhun dan adam kamar Asthma saboda saboda sanyi da qura da aka saba samu a lokacin.

Idan mutum yana son ya kiyaye kansa daga kamuwa daga wadandan cututukan, yana da muhimmanci ya rika amfani da kayayakin abinci masu dauke da sinadaren da ke yaqi da kwayoyin cutar da ke hadasa mura da kuma inganta garkuwar jiki.

Ga wasu daga cikin ababen da ke taimakawa wurin magance mura da alamominta:

Kiwon Lafiya: Nau'oin abinci 7 da za su kare ka daga kamuwa da mura
Kiwon Lafiya: Nau'oin abinci 7 da za su kare ka daga kamuwa da mura
Asali: Twitter

1. Citta

Citta yana daya daga cikin kayan abinci da ke magance mura da alamomin ta. Mutum yana iya fara amfani da shi a cikin shayi ko wani abin sha ko da bai kamu da mura ba.

Wasu bincike da masana su kayi na nuna citta yana maganin mura ne ta hanyar dakile kwayoyin cutar da ke hadasa mura.

2. Barkono

Barkono baya kashe kwayoyin cutar da ke hadasa mura amma yana iya sanya mutum ya samu saukin toshewar hanci. Yana dauke da wani sinadari mai suna capsaicin wadda bincike ya nuna yana washe hancin mutum da kawar da ciwon kai da mura ke sanyawa.

DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya

3. Lemu

Kamar yadda masana suka saba fadi, duk wanda ke son ya rabu da mura toh ya rika samun sinadarin Vitamin C. Duk da cewa ba zai hana mutum kamuwa da mura ba, Vitamin C da ke cikin lemu yana magance alamomin mura da ke takurawa mai fama da ciwon. Lemun tsami, lemun taba da lemu da aka saba sha duk suna dauke da sinadarin.

4. Tafarnuwa

Masana suna kyautata zaton cewa tafarnuwa na dauke da wasu sinadarai masu magance mura amma dai basu gama gano yadda ainihin sindarin da ke magance muran ba a cikin tafarnuwar. Domin magance mura ana iya amfani da tafarnuwa a cikin abinci ko abin sha.

5. 'Ya'yan itatuwa masu yaki da cuta

Binciken masana ya nuna cewa akwai wasu 'ya'yan itatuwa kamar Innibi, Kabeji, Jar albasa. Dukkan wadannan 'ya'yan itatuwan suna dauke da sinadarin da ke yaki da kwayoyin cuta mai suna quercetin da ke yaki da mura.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164