Bakin da Allah ya tsaga: Yadda wata mata ke rayuwa bayan kubuta daga hannun Boko Haram

Bakin da Allah ya tsaga: Yadda wata mata ke rayuwa bayan kubuta daga hannun Boko Haram

Elizabeth Innocent tana daya daga cikin mutanen da suka tsinci kansu cikin wahalhalun rayuwa a jihar Borno sakamakon barnar da 'yan kungiyar Boko Haram suka rika yi a jihar Borno.

Leadership ta ruwaito cewa Elizabeth ta fara sana'ar siyar da fara ne a hanyar Damboa domin ta taimakawa mijinta da yaran ta guda uku domin halin da ta tsinci kan ta a rayuwa.

A ko yaushe tana zuwa wajen aikinta da yamma dauke da tukunya da itace da sauran kayayakin suya domin tabbatar da cewa abokan huldar ta suna gamsuwa da farar da suke saya daga wajen ta.

Yanzu dai ta zama kwarariya a wannnan sana'ar kuma ta ce tana da wani salo na musamman da take suyar ta wadda ya sa abokan huldar ta daga wurare masu yawa suke dawowa su saya fara a duk lokacin da suka ziyarci Borno.

Bakin da Allah ya tsaga: Yadda wata mata ke rayuwa bayan kubuta daga hannun Boko Haram
Bakin da Allah ya tsaga: Yadda wata mata ke rayuwa bayan kubuta daga hannun Boko Haram
Asali: Twitter

Fara yana daya daga cikin abincin da mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya ke ci na tsawon lokaci a matsayin abin marmari ko kuma a saka cikin miya ko abinci.

DUBA WANNAN: Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

"Muna sayan fara ne daga 'yan kabilar Kanuri da suke kamo shi daga kauye. Muna sayo farar daga kasuwar Shagari Locust. Mukan cire fukafukin idan mun tafi gida sai kuma mu tafasa shi kadan. Yayin tafasawar muna saka gishiri da maggi da lemun tsami sannan daga bisani mu sanya a rana ya bushe kuma hakan na daukar kamar kwana guda daya," inji ta.

Duk da cewa wannan sana'ar shine Elizabeth ta ke rike kanta da shi, ta ce ba tayi tsamanin abinda za tayi ba kenan a lokacin da ta iso Borno tare da mijinta daga jihar Benue.

"A lokacin da na fara sana'ar a 2009. Na fara da N1500 ne domin buhun fara N1500 ake sayar da shi kuma a lokacin ana samun alkhairi sosai," inji ta.

Elizabeth da iyalan ta suna lalaba abinda ta ke samu daga sana'ar ta da abinda mijinta ke samu daga shagonsa na sayar da kayayakin lantarki.

A lokacin da mayakan Boko Haram suka fara kawo farmaki cikin Maiduguri, Elizabeth da iyalanta sunyi gudun hijira zuwa Abuja wajen 'yan uwansu amma daga bisani suka dawo saboda rashin aikin yi.

Yanzu rayuwa a Maiduguri akwai wahala saboda barnar da 'yan ta'addan su kayi.

Babu wani aiki da zanyi saboda haka na koma sana'a ta na sayar da fara. Abinda ya fara bani mamaki shine yadda farashin fara ya yi tashin gauron zabi saboda Boko Haram.

"Buhu daya da na saba saya a N1,500 yanzu ya koma N18,000. Kudin ya tashi ne saboda fitintinun da Boko Haram suka haifar. Yawancin 'yan kauyen da ke zuwa daji su kamo fara sun gudu saboda tashe-tashen bam."

Elizabeth ta ce saboda tsadar da fara ya yi, ba ta samun riba kamar yadda ta saba samu a baya.

Mutane da dama da suka saba sayan fara wajen Elizabeth sun bayyana gamsuwar su kan yadda ta ke sarrafa farar ta saboda kwarewa da tayi a aikin.

Kwararu sun bayyana cewa kwari kamar fara suna dauke da sinadarin gina jiki na Protein, fat, Vitamins, fibre da minerals. United Nations Food and Agriculture Organisation (FOA) ta ce a kalla mutane 1 biliyan ne a duniya suke cin kwari a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel