Buhari ya raba gardama a jihar Ogun: Ya zabi daya daga cikin 'yan takarar APC

Buhari ya raba gardama a jihar Ogun: Ya zabi daya daga cikin 'yan takarar APC

- Shugaba Buhari ya raba gardama da akeyi tsakanin Abdulkadir Adekunle Akinlade da Dapo Abiodun a jihar Ogun

- Gwamna mai barin gado, Ibikunle Amosun yana goyon bayan Abdulkadir Adekunle Akinlade amma uwar jam'iyyar ba ta amBuhari ya bayyana dan takarar da ya ke goyon baya a jihar Ogun

- An ruwaito cewa Shugaba Buhari ya zabi Abiodun a matsayin dan takarar gwamna na APC kuma ya yi alkawarin zuwa jihar domin ya gabatar da shi ga al'ummar jihar

A jiya ne shugaba Muhammadu Buhari ya raba gardama da akeyi a kan zaban dan takarar gwamna a jihar Osun sakamakon goyon bayan dan takarar jam'iyyar APC, Dapo Abiodun a wani taro da ya yi da Cif Segun Osoba a fadar Aso Villa da ke Abuja.

Buhari ya raba gardama a jihar Ogun: Ya zabi daya daga cikin 'yan takarar APC
Buhari ya raba gardama a jihar Ogun: Ya zabi daya daga cikin 'yan takarar APC
Asali: Twitter

Gwamna Ibikunle Amosun na jihar Ogun da Shugaban jam'iyyar Allied Peoples Movement (APM), Alhaji Yusuf Dantalle sun gana da shugaban kasar a gidan gwamnati a ranar Litinin.

DUBA WANNAN: Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

Jam'iyyar APM ta goyi bayan Shugaba Buhari a matsayin dan takarar da zata goyi baya a babban zaben 2019. Sai dai gwamna Amosun na jihar Ogun ya fi son dan takarar gwamna na jam'iyyar APM, Abdulkadir Adekunle Akinlade ya gaje shi.

Daily Trust ta ruwaito cewa an dade ana takadamma tsakanin Abiodun da Akinlade a kan neman amincewar Shugaba Buhari.

Cif Osoba ya shaidawa manema labarai a gidan gwamnati cewa Shugaban kasa ya goyi bayan Abiodun kuma ya yi alkawarin kai ziyara jihar Ogun domin ya gabatar da shi ga al'ummar jihar a matsayin dan takarar gwamna.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel