Buhari bai cancanci baƙin cikin rasuwar Marigayi Shagari ba bayan yiwa gwamnatin sa juyin mulki - Junaid

Buhari bai cancanci baƙin cikin rasuwar Marigayi Shagari ba bayan yiwa gwamnatin sa juyin mulki - Junaid

Wani tsohon dan majalisar tarayya Najeriya a gwamnatin jamhuriya ta biyu, Dakta Junaid Muhammad, ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da bayyana baƙin cikinsa kan rasuwar tsohon shugaban kasa, Alhaji Shehu Shagari.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da sanadin kakakin sa, Mista Femi Adesina, ya bayyana baƙin cikinsa dangane da mutuwar tsohon shugaban kasa, Shagari, da ajali ya katse ma sa hanzari a jiya Juma'a.

Da yammacin jiya ta Juma'a, ajali ya cimma tsohon shugaban kasar Najeriya a babban Asitin kasa da ke garin Abuja bayan ya sha fama da wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya duba da yanayi na tsufa.

Buhari bai cancanci baƙin cikin rasuwar Marigayi Shagari ba bayan yiwa gwamnatin sa juyin mulki - Junaid
Buhari bai cancanci baƙin cikin rasuwar Marigayi Shagari ba bayan yiwa gwamnatin sa juyin mulki - Junaid
Asali: Depositphotos

Asali: UGC

Lamarin ya sanya shugaban kasa Buhari tare da dumbin jiga-jigan kasa suka bayyana baƙin cikin wannan babban rashi gami kwarara yabo kan kan kyawawan dabi'u da Marigayi ya dabbaka yayin rayuwar sa. Sun kuma roki Mai Duka akan ya kyatata makwacin sa da rahama a gare sa.

Cikin zayyana jawaban sa yayin ganawa da manema labarai, Dakta Junaidu ya yabawa rayuwar marigayi Shagari da a yayin ta ya samu mafi kololuwar karamci dangane da kyawawan dabi'u na dattako, kana'a da kuma gwagwarmaya da tsayuwa bisa gaskiya da kishin kasa.

Ya ci gaba da cewa, tsagwaran kishin kasa da ta mamaye zuciyar marigayi Shagari ta sanya ya gudanar da salon siyasa da ta yiwa ta sauran 'yan siyasar zamani fintinkau da kece raini.

A kalaman tsohon dan majalisar "su na da masaniya kan mafi akasarin mutane masu ikirarin soyayya ga marigayi Shagari wajen bayyana baƙin cikin su dangane da rasuwar sa da ko shakka ba bu makiya ne a gare sa da suka taka rawar gani wajen durkusar da gwamnatin sa kuma kawowa yanzu sun gaza bibiyar tafarki makamancin ta."

KARANTA KUMA: Ina dalilin Buhari da bai kaddamar da yakin neman zaben sa ba a jihar Zamfara, Yobe ko Borno - Fayose

Da ya ke amsa tambayoyin manema labarai dangane da baƙin cikin da shugaban kasa Buhari ya bayyana kan rasuwar Marigayi Shagari, ya ce ko kadan ba bu gaskiya cikin ta sakamakon yadda ya taka rawa wajen kitsa kutungwilar yiwa gwamnatin sa juyin mulki a shekarar 1984.

Ya kara da cewa, duk wani babatu da shugaba Buhari zai yi a halin yanzu na nuna damuwa ko jajantawa dangane da rasuwar Marigayi Shagari, ko kadan ba bu kamshin gaskiya domin kuwa ba ta kai har zuci ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel