Shugaba Buhari ya gana da dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC a fadar Villa

Shugaba Buhari ya gana da dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC a fadar Villa

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu cewa, a yau Juma'a, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Ogun, Olusegun Osoba, a fadar sa ta Villa da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Kazalika, dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC, Dapo Abiodun, ya halarci wannan ganawa tare da shugaban kasa Buhari a fadar Villa da ke garin Abuja.

Shugaba Buhari ya gana da dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC a fadar Villa
Shugaba Buhari ya gana da dan takarar kujerar gwamnan jihar Ogun na jam'iyyar APC a fadar Villa
Asali: Twitter

Yayin ganawar sa da manema labarai, Mista Osoba ya ce gabatarwa da shugaban kasa Buhari dan takarar kujerar gwamna na jihar sa na daya daga cikin manufofin ziyarar sa zuwa fadar Villa.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi hudubar zaman lafiya a jihar Gombe

Tsohon gwamnan yayin jaddada goyon baya ya na kuma yiwa shugaban kasa Buhari fatan alheri gami da nasara a zaben 2019.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari yau ya kaddamar da yakin neman zabe na jam'iyyar sa ta APC cikin birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel