Garin da suka shafe shekara 10 ba wutan lantarki sun samu wuta

Garin da suka shafe shekara 10 ba wutan lantarki sun samu wuta

Sarkin Ode-Aye a jihar Ondo, William Akinlade ya yabawa mahukuntar kamfanin samar da wutan lantarki na Benin (BEDC) saboda dawowa garin da wutan lantarki.

Mutanen garin sun kwashe tsawon shekaru 10 ba su da wuta saboda bashi da hukumar wuta ke bin su.

Akinlade ya mika godiyarsa ga kamfanin saboda samarwa garin wutar lantarki bayan sun shafe shekaru cikin duhu.

Garin da suka shekara 10 ba wutan lantarki sun samu wuta

Garin da suka shekara 10 ba wutan lantarki sun samu wuta
Source: UGC

DUBA WANNAN: Kungiyar IS ta Al-Baghadadi ta kwaci yanki a Borno, ta kafa tuta

"Muna godiya ga Allah. Bayan lokaci mai tsawo, yanzu mun samu wutar lantarki. Muna godiya ga BEDC. Muna godiya ga shugabani da dukkan ma'aikatan kamfanin. Muna addu'ar Allah ya saka muku da alkhairi. Ba zaku taba rasa haske ba a rayuwarku," inji Sarkin.

A ranar Litinin, Shugaban BEDC na jihohin Ondo/Ekiti, Kunbi Labiyi ya umurci ma'aikatan kamfanin suyi duk mai yiwuwa domin ganin al'ummar Ode-Aye sun samu wutar lantarki daga ranar Kirsimetin 2018.

BEDC ta sanar da shirin ta na samar da wutan lantarki ga al'ummar garin Ode-Aye, wadda yana daya daga cikin manyan garuruwan da ba su da wutar lantarki a yankin Ondo ta kudu bayan gwamnan jihar Rotimi Akeredolu ya bayar da umurnin daukan dukkan matakin da ya kamata domin magance matsalar wutan lantarki a akayi shekaru 12 ana fama da shi a yankin.

A cewar BEDC, kamfanin ta kuma gyra wutan lantarki a wasu sassan jihohin Ekiti da suka dade ba su samun wutar lantarki kwata-kwata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel