Ka fara hukunta masu cin hanci daga cikin hadimanka - Daliban Najeriya ga Buhari

Ka fara hukunta masu cin hanci daga cikin hadimanka - Daliban Najeriya ga Buhari

A yau Juma'a ne Kungiyar Daliban Najeriya na Kasa (NANS) ta yi kira da shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta hukunta mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a gwamnatinsa.

Kungiyar ta kuma bukaci shugaba Buhari ya bayar da umurnin cigaba da binciken zargin rashawa da ake yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje domin ya kare mutuncin Najeriya.

A wata sanarwar da mai magana da kungiyar NANS, Adeyemi Amoo ya bayar a Abeokuta, ya kura cewa akwai bukatar a kawar da dukkan mutanen da ke cikin gwamnatin Buhari da aka gano suna da hannu cikin aikata rashawa.

Ka hukunta barayin gwamnati da ke kusa da kai - NANS ta fadawa Buhari
Ka hukunta barayin gwamnati da ke kusa da kai - NANS ta fadawa Buhari
Asali: Twitter

Amoo ya bayyana mamakinsa kan yadda akayi rufa-rufa game da zargin karbar rashawar Ganduje da sunnan cewa yana yiwa jam'iyya biyaya.

DUBA WANNAN: Wani da ya yiwa kanwarsa mai shekaru 15 ciki a Kano ya dora laifi kan shaidan

"Kawo yanzu, mun lura cewa dukkan wadanda ake bincikarsu a kan tuhumar rashawa mutane ne da suka ki buya a karkashin jam'iyyar APC.

"NANs tana son ta tabbatarwa shugaban kasa cewa muddin ya kawar da idonsa a kan zargin rashawar Ganduje da sauran wadanda ake zargi da rashawa a gwamnatinsa, za mu umurci mambobin mu kada su zabi shugaba Muhammadu Buhari a babban zabe mai zuwa," inji mai magana da NANs

Duk da haka, Amoo ya yabawa shugaba Buhari kan kokarin da ya yi wurin yaki da wasu barayin gwamnati da suka dade suna sace kudin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel