'Yan Boko Haram sun kone makarantun Boko uku a Yobe
Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kone makarantun firamare guda biyu da wani ginin sojoji a cikin kwanaki biyu a jihar Yobe.
An lalata makarantun biyu a wasu hare-hare da mayakan kungiyar suka kai a ranakun 24 da 26 ga watan Disamba a garuruwa Kuka-reta da Katarko, masu nisan kilomita 20 daga garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Mayakan sun kone makarantun firamaren Kuka-reta da Katarko da Ngaurawa da daruruwan 'yan gudun hijira ke halarta.
Lawani Babagana, dagachin garin Kuka-reta, ya ce makarantar firamaren garinsa na da mafi yawan dalibai a cikin ragowar makarantun da aka kone.
"Yanzu bamu da halin da yaran zasu shiga ba idan hutu ya kare," a cewar Babagana.
Alhaji Muhammad Goni, mazaunin garin Katarko, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun taba kona makarantar garin a 2014 kafin gwamnatin ta kammala gyaranta a shekarar 205.
"Abun takaici ne ganin yadda 'yan Boko Haram suka sake kona makarantar garin Katarko. Babu abinda zamu iya yi a kan masu kawo harin don hatta sojoji da ya kamata su kare mu, gudu suke yo idan 'yan Boko Haram sun kawo hari. Dole muka gudu muka bar gidajen mu saboda sojoji ba zasu iya kare mu ba," a cewar sa.
DUBA WANNAN: Zamfara: Buhari ya bawa shugaban rundunar sojin sama umarnin gaggawa
Sai dai mazauna garin Damaturu sun nuna damuwa da yawaitar kai hare-hare kauyukan dake gefen garin, tare da yin zargin cewar mayakan na kungiyar na gwada karfinsu ne kafin su kawo hari babban birnin jihar na Yobe.
"Muna rokon gwamnati ta kara ankarar da jami'an tsaro don su zama cikin shirin tsammanin harin mayakan Boko Haram," a cewar Zanna Suleiman, mazaunin garin Damaturu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng