Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku

- Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Buhari, Festus Keyamo ya mayar da martani ga Atiku Abubakar kan cewa gwamnatin Buhari bata yaki da rashawa

- Keyamo ya ce idan da hukumomin Najeriya suna aiki yadda ya kamata da Alhaji Atiku Abubakar yana garkame a gidan yari

- Keyamo ya ce Atiku yana daga cikin manyan wadanda suka amfana da gwamnatin da ta gaza magance rashawa

Kungiyar yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari ta ce idan da Najeriya na kan tsarin gaskiya da tuni dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party Atiku Abubakar yana cikin kurkuku.

Mai magana da yawun kungiyar ta yakin neman Buhari, Festus Keyamo ya ce idan da ace abubuwa na tafiya dai-dai a kasar kafin shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki a 2015 da tuni Atiku yana zaune a gidan yari a maimakon neman takarar shugabancin kasa.

Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku
Da ana kan tsarin gaskiya a Najeriya da tuni kana kurkuku - Buhari ya caccaki Atiku
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Shehu Sani ya lissafo dalilai 3 da yasa manyan Arewa su kayi gum a kan yawaitar kashe-kashe a yankin

"An janyo hankalin mu kan wani da akace dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar ya fadi na kin amincewa da maganar da shugaba Buhari ya yi na cewa hukumomin Najeriya suna barin rashawa na karuwa saboda rashin magance rashawar cikin gagawa.

"Alhaji Atiku ya kuma zargi shugaba Muhammadu Buhari da kawar da idonsa ga wasu abubuwa masu alaka da rashawa da suka faru a karkashin gwamnatinsa.

"Muna son mu tunawa Atiku Abubakar cewa yana daya daga cikin wadanda suka amfana da gwamnatin da ta gaza magance rashawa da ke mulki kafin shugaba Muhammadu Buhari ya karbi mulki a 2015.

"Idan da abubuwa suna tafiya dai-dai, da Alhaji Atiku Abubakar bai saya hannun jarin da ya saya a INTELS a lokacin yana jami'in Kwastam wadda hakan ya sabawa doka. Waddan hannun jarin na 'yan Najeriya ne."

"Idan da Najeriya tana kan tsari ne da tuni an kule Alhaji Atiku Abubakar saboda aikata rashawa da amfani da ofishinsa wajen aikata laifuka bayan da ya sauka daga mulki a matsayin mataimakin shugaban kasa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel