Mu na tare da Shugaba Buhari da Gwamna Bello a 2019 inji Miyetti Allah
Mun ji cewa Kungiyar nan ta Makiyayan Najeriya watau “Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria” ta zabi Muhammadu Buhari a matsayin ‘Dan takarar ta na shugaban kasa a zabe mai zuwa na 2019.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, shugaban kungiyar ta Miyetti Allah na kasa baki daya, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru, ya tabbatar da cewa sun tsaida Buhari a matsayin wanda za su marawa baya.
Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru, yayi wannan jawabi ne a jiya Ranar Laraba a wajen wani taro na Fulani da aka shirya a Garin Minna, cikin Jihar Neja. Shugaban Makiyayan ya kuma ce su na tare da Gwamna Abubakar Sani Bello.
KU KARANTA: Wani Sanata ya caccaki Buba Galadima, ya ce Buhari zai lashe zaben 2019
Shugaban kungiyar ta MACBAN yayi karin haske game da wannan mataki da su ka dauka, inda yace sun yi wa Muhammadu Buhari mubaya’a ne saboda manufofin gwamnatin sa na ganin an gina wuraren kiwon dabbobi a fadin Najeriya.
Kungiyar ta Miyetti Allah ta kara da cewa shugaba Buhari da Gwamnan Jihar Neja watau Sani Bello sun kawo tsare-tsaren da su ka taba rayuwar talakawan kasar nan. Muhammad Kiruwa yace don haka dole su nemi gwamnatin su ta zarce.
Alhaji Kiruwa yake cewa gwamnatin nan mai-ci, tana bakon kokari wajen ganin an shawo kan rikicin da ake yi tsakanin Makiyaya da Manoma Wannan ya sa shugaban kungiyar ya nemi mutanen sa su zabi Buhari da Bello a zaben 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng