An yi ‘yar rigima a tsakanin Magoya-bayan APC da PDP a fadar Sarkin Ilorin

An yi ‘yar rigima a tsakanin Magoya-bayan APC da PDP a fadar Sarkin Ilorin

- Magoya bayan PDP da APC sun yi rikici a fadar Sarkin Ilorin a Jihar Kwara

- Masu marawa Bukola Saraki baya ne su kayi wa ‘Dan takarar APC ihu a fadar

- Wannan ya sa Magoya bayan jam’iyyar APC su kayi kokarin maida martani

An yi ‘yar rigima a tsakanin Magoya-bayan APC da PDP a fadar Sarkin Ilorin

Saraki ya wanke kan sa daga hatsaniyar da aka yi a Garin Ilorin
Source: Twitter

An gamu da ‘yar hatsaniya a fadar Mai martaba Sarkin Ilorin inda rikici ya nemi ya kaure tsakanin Magoya bayan Jam’iyyar APC da kuma wadanda su ke tare da Jam’iyyar PDP a bangarem shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Yayin da ake wani babban taro a Ranar Kirismeti a fadar Sarkin Ilorin, an samu matsala lokacin da ‘Dan takarar APC ya tashi zai yi jawabi amma Magoya bayan Bukola Saraki su ka hana sa ta-cewa inda su ka rika faman ihu a cikin fadar.

Kafin nan, shugaban karamar hukumar Ifelodun, Fatai Ajidagba ya bada gudumuwar kudi a wajen taron, da aka zo kan Abdulrahman Abdulrazak wanda yake neman gwamnan jihar Kwara a karkashin jam’iyyar PDP, sai aka soma ihu.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari ta ba mutane kunya a Najeriya – Bukola Saraki

Magoya bayan Bukola Saraki sun rika kiran “Sai leader, Sai Bukki, Sai Atunwa" a lokacin da Alhaji Abdulrahman Abdulrazak ya mike zai yi jawabi. Su kuma wadanda ke goyon bayan ‘Dan takaran na APC sun maida martani a nan take.

Mutanen na Jam’iyyarAPC sun yi wa Masoyan Bukola Saraki raddi inda su ka rika fada da Yarbanci su na cewa “O to ge!!”, ma’ana “Mun gaji, ya ishe mu haka!” Daga nan ne rikici ya nemi ya kaure inda fadar Sarkin ta kidime da hayaniya.

Wadanda su ka shirya wannan taro sun yi yunkurin natsar da jama’a, amma abin bai yiwu ba. Jaridar Punch ta rahoto cewa bayan lamarin ya ci tura ne sai Mai martaba Sarki Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari ya tashi cikin fushi ya cice daga fadar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel