Hausawa mazauna Legas sun yiwa Osinbajo albishir

Hausawa mazauna Legas sun yiwa Osinbajo albishir

A cigaba da yakin neman zabe shekarar 2019 da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke yi gida-gida, ya ziyarci Alhaji Musa Dogonkadai, sarkin kabilar Hausawa mazauna Agege a garin Legas.

Yayin ziyarar ta Osinbajo, kabilar Hausawan sun yi masa albishir din cewar zasu goyi bayan takarar Buhari da jam'iyyar APC a kyauta, saboda suna jin dadin gwamnatin nan.

Dogonkadai da ragowar al'ummar Hausaw sun tarbi Osinbajo cikin murna da biki yayin da ya isa fadar sarkin a Agege.

Osinbajo ya isa fadar sarki Dogonkadai da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Lahadi kuma ya yi ganawa ta tsawon mintuna 45 da shugabannin kabilar Hausawan yankin.

Ma'ajin al'ummar Hausawa a Agege, Alhaji Abdulkareem, ya ce sun yi matukar farinciki da ziyarar ta mataimakin shugaban kasa.

Hausawa mazauna Legas sun yiwa Osinbajo albishir

Osinbajo a fadar sarkin Hausawa dake Agege a Legas
Source: Twitter

Sannan ya yi masa albishir din cewar zasu zazzagawa jam'iyyar APC kuri'u a zaben shekarar 2019 a kowanne mataki.

"Mun ji dadin ziyarar mataimakin shugaban kasa zuwa wannan fada ta kabilar Hausawan Agege.

DUBA WANNAN: Sanata Wamako ya yi yayyafin kudi ga magoya bayansa, hotuna

"Muna jin dadin wannan gwamnatin. Bama bukatar kudi; kwanciyar hankali da zaman lafiya muke so, kuma mun same su a wannan gwamnatin. Akwai zaman lafiya a Agege da jihar Legas bakidaya.

"Saboda muna son cigaba da zama lafiya da cin moriyar aiyukan da wannan gwamnatin ke yi zamu zabi jam'iyyar APC ne a zaben shekarar 2019 a kowanne mataki," a jawabin ma'ajin.

Daga cikin tawagar Osinbajo yayin ziyarar da ya kai akwai Sanata Babafemi Ojudu, mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin siyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel