Hakkin makobtaka: Sarkin Musulmi ya taya Kiristoci murnar kirsimeti

Hakkin makobtaka: Sarkin Musulmi ya taya Kiristoci murnar kirsimeti

Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli na harkokin addinin musulunci (NSCIA), Alhaji Sa'ad Muhammad Abubakar ya mika sakon taya murnar bikin Kirsimeti ga dukkan mabiya addinin Kirista a Najeriya.

Wannan sakon yana dauke ne cikin wata wasika da ya aike wa shugaban kungiyar mabiya addinin kirista na Najeriya (CAN), Dr. Samson Olasupo Ayokunle.

Wasikar da ke dauka da sa hannun mataimakin sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu ya ce kungiyar NSCIA tana taya 'yan uwanmu Kirista murnar Kirsimeti na shekarar 2018.

Hakkin makobtaka: Sarkin Musulmi ya taya Kiristoci murnar kirsimeti

Hakkin makobtaka: Sarkin Musulmi ya taya Kiristoci murnar kirsimeti
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Karin aure da manoma keyi ya janyo hayayafar al'umma a Najeriya - Minista

"A yayin da kuke murnar zagayowar wannan ranar mai muhimmanci, al'ummar musulmi suna muku fatan Allah ya yi muku jagora ya saka albarka a bikin," inji Shehu.

A cewarsa, bikin na tun ranar haihuwar Annabi Isa (AS) wata dama ce da 'yan Najeriya suka samu na mika godiyarsu ga Allah da kuma sake yiwa kasa addu'a domin samun zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan kasar.

"A yayin da kuke addu'o'i da shagali, za mu cigaba da rokon Allah ya bawa Najeriya ikon magance kallubalen da ta ke fuskanta ya kuma bamu ikon gudanar da sahihiyar zaben cikib zaman lafiya a watannin da ke tafe.

"Annabi Isa yana daya daga cikin Annabawa masu daraja da dukkan musulmi ke girmamawa. A Kuran'ani mai girma Allah ya ambaci sunansa sama da 25 (Q. 2:87; 2:136; 2:253; 3:45; 3:52; 3:55; 3:59; 3:84; 4:157; 4:163; 4:171….).

(Duk da cewa akwai banbancin fahimta a kansa tsakanin musulmi da kirista, hakan bai hana shi kasancewa abin koyi ga dukkan mabiya addinan biyu ba.

"A yayin da miliyoyin kirista a kasar mu ke murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Isa, muna addu'a wannan bikin zai karfafa mana imani, kaunar juna, halaye na gari, yafiya da sauran halayensa. Muna kira ga dukkan 'yan Najeriya suyi koyi da halayensa da na sauran annabawa na gaskiya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel