Albashin Dariye: SERAP ta maka Saraki a kotu

Albashin Dariye: SERAP ta maka Saraki a kotu

Kungiyar SERAP mai rajin yaki da cin hanci da tabbatar da mulkin gaskiya a Najeriya ta maka shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki, a kotu a kan cigaba da biyan tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, albashi.

A cikin jawabin da kungiyar SERAP ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta ce ta kai Saraki kara ne domin a tilasta masa dakatar da biyan Sanata Dariye albashi tunda yanzu haka yana tsare a gidan yari, kuma ba wani aiki yake yi da za a ke biyansa albashi ba.

Lauyar kungiyar ta shaidawa majiyar Legit.ng cewar ta shigar da karar Saraki ne a gaban wata kotun gwamnatin tarayya dake Legas. SERAP ta ce majalisar dattijai na biyan Sanata Dariye albashin naira 750 da wasu alawus-alawus har na miliyan 13.5 duk wata alhalin yana tsare a gidan yari.

Albashin Dariye: SERAP ta maka Saraki a kotu

Saraki
Source: Depositphotos

A nata bangaren, majalisar ta dattijai ta ce bata da wata hujja da zata dogara da ita wajen dakatar da albashi da alawus din Sanata Dariye.

Majalisar ta ce har yanzu Dariye na nan a matsayinsa na Sanata kuma zai ci gaba da cin moriyar duk wani alfanu da takwarorinsa Sanatoci ke cin moriya.

DUBA WANNAN: 2019: INEC ta sake bullo da dabarun magance magudin zabe

Mohammed Isah, mai taimakawa Saraki a bangaren yada labarai, ya shaidawa majiyar mu cewar, "ba a rubutowa majalisa takarda daga ofishin ministan shari'a a kan cewa an yanke wa Dariye hukunci ba don haka a dakatar da albashi da alawus dinsa ba tunda yana gidan yari."

Tun a watan Yuni ne wata kotun gwamnatin tarayya ta yanke wa Sanata Dariye hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bayan samun sa da laifin cin hanci da rashawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel