Taron dangi: Matar Atiku ta zargi Buhari da kashe 'yan Najeriya da yunwa

Taron dangi: Matar Atiku ta zargi Buhari da kashe 'yan Najeriya da yunwa

Titi Abubakar, uwargidan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ta bayyana rashin jin dadin ta a kan halin da al'ummar Najeriya ke ciki a halin yanzu musamman mutanen yankin Arewa.

A yayin da uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta zargi na kusa da Buhari laifi a kan yadda abubuwa ke tabarbarewa a kasar, Titi Abubakar tayi korafi ne a kan yadda talauci ke karuwa da rashin ayyukan yi da rashin lafiya da ke janyo al'umma na mutuwa.

Titi ta koka kan yadda a yanzu 'yan Najeriya suke gaza sayan kayayakin masarufi da abinci idan aka kwantanta da yadda lamura ke tafiya gabanin zuwan shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2015 wadd ta ce abin kunya ne.

Taron dangi: Matar Atiku ta zargi Buhari da kashe 'yan Najeriya da yunwa

Taron dangi: Matar Atiku ta zargi Buhari da kashe 'yan Najeriya da yunwa
Source: UGC

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta fadi abinda ke janyo hare-haren ta'addanci a Zamfara da Kaduna

"Muna cikin mawuyacin hali. Ku manta labarai da hotunan da kuke gani a kafafen watsa labarai. Dukkansu karerayi ne da dabarbaru.

"Ku tafi kudu maso gabas ku ga yadda zaizayar kasa ya yi barna sosai. Wasu wuraren kai kace iskar Tsunami ne tayi barna a wurin.

"Tituna da yawa sun lalace har ta kai ga cewa keke da babur ba su iya bin hanyoyin. Daukan masu ciki a amalanke zuwa asibiti yayin nakuda ya zama ruwan dare," inji ta.

Kazalika, ta yi tsokaci a kan "matsananciyar talauci da tayi katutu a arewacin Najeriya," inda ta ce talauci yana kashe mutane fiye da 'yan ta'adda a yankin arewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel