Zan rika biyan Matasan Neja 20000 idan na zama Gwamna – Nasko

Zan rika biyan Matasan Neja 20000 idan na zama Gwamna – Nasko

Mun samu labari daga wata Jaridar Najeriya cewa wani ‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben 2019, yayi alkawarin cewa zai rika biyan Matasan Jihar sa kudi kowane wata idan har aka zabe shi.

Zan rika biyan Matasan Neja 20000 idan na zama Gwamna – Nasko

Mai neman Gwamna Jihar Neja a PDP Umar Nasko wajen wani gangami
Source: Facebook

‘Dan takarar Gwamnan Jihar Neja a karkashin Jam’iyyar PDP, Alhaji Umar Mohammed Nasko ya sha alwashin biyan Matasa wadanda su ka kamalla karatu kuma su gaza samun sana’a N20, 000 a kowane wata, da zarar ya zama Gwamna.

Umar Nasko yace zai kawo wani tsari na musamman da zai ragewa al’umma radadin talauci idan ya samu darewa a kan karagar mulki. Alhaji Nasko ya bayyana wannan ne lokacin da yake yawan yakin neman zabe a cikin Garin Suleja.

KU KARANTA: Shugaban kasa Buhari ya fadawa ‘Yan Najeriya wanda za su zaba a 2019

Alhaji Nasko ya soki Gwamnatin APC wanda yace ta gaza kawo wani tsari da zai yi maganin marasa aikin yi da ake da su a cikin gari. Nasko yace idan har mutane su ka zabi PDP a 2019, yana da tsari a kasa da zai samawa jama’a aikin yi.

Haka zalika ‘Dan takarar Gwamnan ya soki Gwamna Abubakar Bello a dalilin soke tsarin karatu da aka saba yi a Jihar kyauta. Nasko yace wannan mataki da Gwamnan mai-ci ya dauka ya haddasawa Jihar Neja koma-baya na shekaru da dama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel