An kone motocin yakin neman zabe Buhari 2 a jihar PDP

An kone motocin yakin neman zabe Buhari 2 a jihar PDP

- Wasu mutane, da ba a san ko su waye ba, sun kai hari ofishin yakin neman zaben daya daga cikin masu ikirarin takarar gwamna a APC a jihar Enugu

- Dan takarar, George Tagbo Ogara, ya ce wadanda suka kai harin sun yi amfani da abubuwa masu fashewa wajen kai harin

- Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Enugu, Ebere Amaraizu, ya tabbatar da labarin kai harin tare da bayyana cewar suna gudanar da bincike

An kone wasu motocin yakin neman zaben jam'iyyar APC masu dauke da hotunan Buhari/Osinbajo a ofishin kamfen din George Tagbo Ogara, daya daga cikin masu ikirarin takarar gwamnan jihar Enugu, a karkashin jam'iyyar APC.

A daren jiya, Asabar, ne wasu matasa da ba a san ko su waye ba suka kai harin ofishin Ogara.

Majiyar legit.ng ta ce da kyar jami'an hukumar kashe gobara suka shawo kan wutar dake ci a ofishin da matasan suka kai harin.

An kone motocin yakin neman zabe Buhari 2 a jihar PDP

Motocin yakin neman zabe Buhari
Source: Depositphotos

Da yake magana a kan harin da aka kai, Ogara ya ce wadanda suka kai harin sun yi amfani da sindarai masu fashewa (IEDs) wajen kone motocin.

"Sun kai harin ne ta hanyar amfani da sinadarai masu fashewa. Babu abinda ni ko wani farar hula zai iya a kan lamarin, jami'an 'yan sanda da na DSS zasu gudanar da bincike a kan lamarin," a cewar Ogara.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka daina goyon bayan Atiku - shugaban kungiyoyi 145

Yanzu haka wata kotun Abuja ta saka ranar 10 ga watan Janairu domin yanke hukunci a kan karar da Ogara ya shigar bayan jam'iyyar APC ta mika sunan tsohon sanata, Ayogu Eze, ga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a matsayin dan takararta na gwamna a jihar Enugu.

Hukumar 'yan sanda, ta bakin kakakinta a jihar Enugu, Ebere Amaraizu, ta tabbatar da labarin kai harin tare da bayyana cewar suna gudanar da bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel