Kwanya: Diyar Hausawa ta kafa tarihi a tsangayar kimiyya a jami'ar Sokoto

Kwanya: Diyar Hausawa ta kafa tarihi a tsangayar kimiyya a jami'ar Sokoto

Zainab Bashir, wata daliba 'yar asalin jihar Katsina, ta kafa tarihi a tsangayar kimiyya bayan ta samu mafi yawan maki a tarihin sashen karatun Physics a jami'ar Usman Danfodio (UDUS) dake Sokoto.

Zainab ta kammala karatun digiri da jimillar maki 4.87 cikin maki 5.00 da dalibi zai iya samu a karatun digiri.

'Yar asalin jihar Katsina, Zainab tayi bajintar da ba a taba yi ba a bangaren karatun Physics a jami'ar ta UDUS.

Matashiyar ta ce tun tana makarantar sakandire take matukar kaunar Physics kuma tayi farinciki da aka bata gurbin karantar sa a jami'a.

Kwanya: Diyar Hausawa ta kafa tarihi a tsangayar kimiyya a jami'ar Sokoto

Zainab Bashir
Source: Depositphotos

"Zabina na farko shine na karanta likitanci amma sai Allah ya yi min canji da abinda na fi kwarewa da shi tun daga makarantar sakandire. Ban taba tsoro ko ganin wahalar lissafin Physics ba," a cewar Zainab.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa muka daina goyon bayan Atiku - shugaban kungiyoyi 145

Da take bayanin yadda ta iya samun nasarar tsira da sakamako mai kyau haka ba tare da samari sun rudeta ba, Zainab ta ce sa'ar ta daya ta riga ta fitar miji, a don haka samari basu wani dauke mata hankali ba lokacin karatun ta a UDUS.

Kwanya: Diyar Hausawa ta kafa tarihi a tsangayar kimiyya a jami'ar Sokoto

Sakamakon Zainab
Source: Depositphotos

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel